Babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG a takaice, ya gudanar da bikin musayar al’adu, na murnar cika shekaru 20 da kafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni a tsakanin kasashen Sin da Italiya a jiya Litinin 14 ga watan nan a birnin Milan, inda aka kaddamar da shirye-shiryen bidiyo da na intanet masu yawa, karkashin hadin kan kasashen biyu.
Baya ga haka, CMG ya kuma soma aiwatar da hadin kai tare da jaridar Milano Finanza, da kamfanin Telespazio na Italiya da dai sauransu. (Bilkisu Xin)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp