An gudanar da wasanni a Urumqi, babban birnin jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta dake arewa maso yammacin kasar Sin jiya da dare, domin murnar cikar gammayar kungiyar musammam mai aikin raya tattalin arzikin jihar Xinjiang shekaru 70 da kafuwa.
Mataimakin firaministan Sin He Lifeng, kuma mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS ne ya jagorancin wata tawaga domin kallon wasannin tare da mutanen mabambantan kabilu daga dukkan bangarorin rayuwa.
- NITDA Za Ta Wayar Da Kan Al’umma Kan Sha’anin Tsaro Ta Intanet
- NITDA Za Ta Wayar Da Kan Al’umma Kan Sha’anin Tsaro Ta Intanet
Wasannin sun bayyana gagarumin ci gaban da gammayar kungiyar musammam mai aikin raya tattalin arzikin jihar Xinjiang ta samu cikin shekaru 70 da suka gabata.
A nasu bangare, kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, da majalisar gudanarwar kasar, gami da kwamitin aikin soja na tsakiya ta kasar, su ma sun tura wa kungiyar raya tattalin arzikin jihar Xinjiang sako don taya murnar bikin ranar kafuwarta. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)