Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Ƙasa (NITDA) za ta jagoranci taron wayar da kan al’umma kan sha’anin tsaro ta Intanet na shekara shekara (NCSAM) a cikin wannan wata na Oktoba, da nufin bunƙasa hanyoyin wayar da kan al’umma dangane da harkokin tsaron intanet a faɗin ƙasar nan.
Gangamin na tsawon wata guda za a yi shi ne domin ilimantar da ɗaiɗaikun mutane da ƙungiyoyi kan muhimman hanyoyin tsaro ta intanet, barazanar da ake fuskanta, da kuma hanyoyin matakan kariya.
- ICPC Ta Ƙulla Yarjejeniyar Haɗin Gwuiwa da Wata Hukuma A London
- ICPC Da NITDA Sun Kulla Alakar Aiki Don Yaki Da Rashawa Ta Hanyar Fasaha
Taken taron na bana shi ne, “Samun Aminci A Yau, Domin Kariya A Gobe,” domin jaddada muhimmancin ɗaukar matakan kariya cikin ƙwazo don kiyaye barazanar da ake fuskanta ta yanar gizo wacce ke ƙaruwa da ta’azzara.
A tsawon wannan wata, NITDA za ta mayar da hankali wajen bai wa ‘yan ƙasa da ‘yan kasuwa kayan aiki da kuma ilimin da suka dace domin inganta ayyukansu ta fuskacin tsaro.