A ranar Asabar ne aka yi garkuwa da iyayen dan wasan Liverpool Luis Diaz a Colombia.
Dan wasan na Liverpool ya samu labari a ranar Asabar cewa an yi garkuwa da iyayensa, Luis Manuel Díaz da mahaifiyarsa Cilenis Marulanda daga wani gidan mai a garinsu na Barracas dake Colombia.
- Shin Salah Zai Iya Barin Liverpool Zuwa Gobe?
- Manchester United Zata Karbi Bakuncin Brentford A Filin Wasa Na Old Trafford
Sai dai hukumomin yankin sun ceci mahaifiyar Luis Diaz, sakamakon wani shingen binciken da ‘yan sandan yankin suka kafa.
Amma har yanzu da ake wannan rahoton ba a kubutar da mahaifinsa ba.
An tabbatar da cewa, shugaban kasar Colombia Gustavo Petro ne ya ba da labarin ceto mahaifiyar Diaz a shafinsa na X.
Iyayen Diaz suna tafiya ne zuwa unguwar Los Olivos a cikin wata motar da suka mallaka ranar Asabar kafin a kawo musu hari har a yi garkuwa da su.
Diaz shi ne babban dan wasa a kasar Colombia kuma ya zura kwallaye tara a wasanni 43 daya bugawa kasar.