Yau Alhamis, cibiyar yaki da shan maganin kara kuzari yayin wasanni ta Sin ta fitar da wata sanarwa cewa, bisa la’akari da “danyun ayyukan” da Amurka ta yi a fannin wasan guje-guje da tsalle-tsalle, akwai bukatar hukumar yin bincike ta (ITA), da ta kara yawan bincike game da shan maganin kara kuzari tsakanin ’yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na Amurka, yayin gasar wasannin Olympics ta Paris, ta yadda za a kare halastattun iko da moriyar ’yan wasa dake bin doka na kasashe da yankuna daban daban, da kuma sake karfafa kwarin gwiwar ’yan wasan duniya kan takara bisa adalci. (Safiyah Ma)
Talla