• English
  • Business News
Tuesday, November 4, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Yi Kira Da Aiwatar Da Matakan Samar Da Ilimi Mai Inganci A Nahiyar Afirka

by CGTN Hausa
1 year ago
Afirka

Kungiyar tarayyar Afirka ta AU da jami’ai daga bangaren kasar Sin, sun yi kira da a kara azama wajen aiwatar da matakan samar da ilimi mai inganci a sassan nahiyar Afirka, ta yadda hakan zai baiwa nahiyar damar cimma nasarar sauya salon tattalin arziki da zamantakewar al’ummunta.

An yi kiran ne a jiya Juma’a a birnin Addis Ababa, fadar mulkin kasar Habasha, yayin taron tattaunawa na hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka game da raya ilimi.

  • Gwamnonin Arewa-Maso-Yamma Sun Nemi Goyon Bayan MDD Kan Magance Ƙalubalen Yankin
  • Kamfanin Metrodigital Zai Kalubalanci Mamayar Multichoice A Fagen Talabijin

Taron ya kuma mayar da hankali ga zakulo hanyoyin da kasar Sin za ta iya taimakawa nahiyar Afirka da su, ta yadda nahiyar za ta kai ga cimma manufar ci gaba mai dorewa ta MDD ko SDGs, da ma kudurorin dake cikin ajandar bunkasa nahiyar ta kungiyar AU na shekaru 50, wadanda ake fatan cimmawa nan zuwa shekarar 2063.

Da yake tsokaci yayin taron, kwamishinan AU mai lura da harkokin ilimi, kimiyya da fasaha, da kirkire-kirkire Mohammed Belhocine, ya ce ilimin fasahohi da na koyon sana’o’i, na taka muhimmiyar rawa ga cimma nasarar ajandar SDGs, da ta nahiyar Afirka ta nan zuwa shekarar 2063, don haka ya yi kira ga kasar Sin, da ta kara fadada bayar da horo a sassan Afirka, a fannonin koyon sana’o’in hannu da horaswa, kana ta horas da matasan nahiyar ilimomi, da sanin makamar aiki, da za su ba su damar baiwa kasashensu gudummawar raya tattalin arziki.

A nasa bangare kuwa, shugaban tawagar Sin a AU Hu Changchun, cewa ya yi a matsayinta na babbar abokiyar hadin gwiwar nahiyar Afirka bisa manyan tsare-tsare daga dukkanin fannoni, kasar Sin na matukar goyon bayan AU, a shirinta na cimma nasarar muradunta, tana kuma karfafa hadin gwiwa da nahiyar a fannin raya ilimi, da bangaren samar da kwarewa. (Saminu Alhassan)

LABARAI MASU NASABA

Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin

Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin

November 3, 2025
Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce

November 3, 2025
An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau
Daga Birnin Sin

An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau

November 3, 2025
Next Post
Za A Fara Rabon Takin CBN Kyauta, Sai Dai Masana Sun Ba Da Shawara

Za A Fara Rabon Takin CBN Kyauta, Sai Dai Masana Sun Ba Da Shawara

LABARAI MASU NASABA

China Ta Gargaɗi Amurka Kan Tsoma Baki A Harkokin Nijeriya

China Ta Gargaɗi Amurka Kan Tsoma Baki A Harkokin Nijeriya

November 4, 2025
2023: Me Ya Sa Ake Rububin Wike?

Atiku Ya Fice Daga PDP Saboda Na Ƙi Bari Ya Lalata Mana Jam’iyya – Wike

November 4, 2025
Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Ba Su Goyi Bayana Ba Lokacin Da Aka Dakatar Da Ni – Natasha

Dalilin Da Ya Sa Sanatoci Ba Su Goyi Bayana Ba Lokacin Da Aka Dakatar Da Ni – Natasha

November 4, 2025
Kalaman Trump A Kan Nijeriya Abun Damuwa Ne – Peter Obi 

Kalaman Trump A Kan Nijeriya Abun Damuwa Ne – Peter Obi 

November 4, 2025
Jami’an Tsaro Sun Dawo Da Fasfo Ɗin Sanata Natasha Bayan Ƙwace Shi A Abuja

Natasha Ta Zargi Akpabio Da Sanya Jami’an Tsaro Su Ƙwace Mata Fasfo A Filin Jirgin Saman Abuja 

November 4, 2025
Masu Kashe Mutane A Kudu Maso Gabas Kiristoci Ne – Soludo

Masu Kashe Mutane A Kudu Maso Gabas Kiristoci Ne – Soludo

November 4, 2025
Ribadu Ya Gana Da Hafsoshin Tsaro Biyo Bayan Kalaman Trump 

Ribadu Ya Gana Da Hafsoshin Tsaro Biyo Bayan Kalaman Trump 

November 4, 2025
Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin

Sarkin Kasar Spaniya Zai Kawo Ziyara Kasar Sin

November 3, 2025
Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce

Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Trump Dangane Da Gwajin Nukiliya A Asirce

November 3, 2025
An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau

An Bude Taron Kasuwanci Na Duniya Na 18 A Macau

November 3, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.