Tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA, Sepp Blatter ya ce an tafka babban kuskure wajen bai wa Qatar damar karbar bakuncin gasar lashe kofin duniya ta bana da za a fara a wannan watan.
Blatter, mai shekaru 86 a duniya, shike shugabantar hukumar FIFA lokacin da aka baiwa Qatar dammar karbar bakuncin gasar a shekarar 2010 kuma tun bayan bata wannan damar Kasar ke shan suka game da matsayar ta na hana masu auren jinsi gudanar da mu’amular su a lokacin gasar, da kuma zargin cin zarafin ma’aikata ‘yan cirani a kasar.
Blatter ya ce Qatar karamar kasa ce, gasar lashe kofin duniya ya mata girma ta amshi bakuncin sa sannan ya ce ko a lokacin zaben, Amurka ya zaba, sai dai ya dora alhakin bai wa Qatar damar daukar nauyin gasar a wuyan tsohon shugaban hukumar kwallon kafar Turai Michel Platini.
Wannan ne karo na farko da wata kasa daga yankin gabas ta tsakiya ke samun damar karbar bakuncin gasar a cikin shekaru 92 duk da kasancewar kasashen nahiyar a matsayin ‘yan gaba-gaba da ke zuba makudan kudi a abin da ya shafi kwallon kafa sannan wannan ne karon farko da za a gudanar da wannan gasa a yanayin hunturu.