Mutum daya ya rasu yayin da matasan gari suka yi taho mu gama da ‘yan bindiga lokacin kai hari garin Kware a Jihar Sokoto a daren Asabar. Shaidu sun bayyana cewa, ‘yan bindigar sun shiga garin Kware, cibiyar karamar hukumar Kware, da nufin aikata fashi.
Mamba na kungiyar masu samar da tsaro ta cikin gari, Bello Mai Maciji, ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun samu nasarar satar wani adadin kudi daga hannun Dan Balgore, wani sanannen mai kasuwanci a yankin.
- Yadda Sakamakon Jawo Jarin Waje A Rubu’in Farko Na Bana Ya Ba Da Sha’awa A Kasar Sin
- Nijeriya Ta Biya Bashin Ɗaliban Da Ke Karatu A Ƙasashen Waje
Mai Maciji ya bayyana cewa, ‘yan fashin sun bayyana cewa suna da masaniya game da kudin kasuwancin da yake dauke da shi a cikin motarsa, lokacin da suka kai harin yayin da Balgore ya tsaya a cikin garin don sayen abinci. Mai Maciji ya kara da cewa, mutumin da ya mutu ya rasu ne bayan ya ji raunukan harbi yayin harin.
Duk da haka, Mai Maciji ya bayyana cewa ‘yan bindigan sun gudu lokacin da matasan gari suka afka musu. Sun kona wani shago a kasuwar, amma wutar ba ta bazu zuwa sauran shaguna ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp