Mutum ɗaya ya rasu yayin da matasan gari suka yi taho mu gama da ‘yan bindiga lokacin kai hari garin Kware a Jihar Sokoto a daren Asabar. Shaidu sun bayyana cewa, ‘yan bindigar sun shiga garin Kware, cibiyar ƙaramar hukumar Kware, da nufin aikata fashi.
Mamba na ƙungiyar masu samar da tsaro ta cikin gari, Bello Mai Maciji, ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun samu nasarar satar wani adadin kudi daga hannun Dan Balgore, wani sanannen mai kasuwanci a yankin.
- Gwamnatin Sakkwato Ta Siyawa ‘Yan Gudun Hijira Gidan Miliyan 100
- ‘Yan Bindiga A Ƙarƙashin Jagorancin Turji Sun Kashe Manoma 12 A Sokoto
Mai Maciji ya bayyana cewa, ‘yan fashin sun bayyana cewa suna da masaniya game da kuɗin kasuwancin da yake ɗauke da shi a cikin motarsa, lokacin da suka kai harin yayin da Balgore ya tsaya a cikin garin don sayen abinci. Mai Maciji ya ƙara da cewa, mutumin da ya mutu ya rasu ne bayan ya ji raunukan harbi yayin harin.
Duk da haka, Mai Maciji ya bayyana cewa ‘yan bindigan sun gudu lokacin da matasan gari suka afka musu. Sun kona wani shago a kasuwar, amma wutar ba ta bazu zuwa sauran shaguna ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp