Hukumar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA ta bayyana cewa, jami’anta sun kwace kilo 8,852 na Tabar Wiwi (Cannabis)
Kakakin hukumar Femi Babafemi ne ya bayyana hakan a ranar Laahdi a cikin sanarwar da ya fitar, inda ya ce, jami’an sun samu wannan nasarar ce, biyo bayan samun bayanan sirri.
Ya ce, jami’n sun yiwa masu safarra miyagun kwayoyin ne kwanton Bauna a kan titin Eleko Beach da ke Lekki cikin jihar Legas da misalign karfe 4:51 na safiyar ranar Alhamis din da ta gabata.
A cewarsa, jami’an sun yi musayar wuta da ‘yan bindigan da suka rako masu safarar haramtaccen kayan cikin manyan motoci biyu na kusan tsawon mintuna 30.
Femi ya bayyana cewa, jami’an NDLEA sun samu babbar Nasara kan masu rakiyar haramtattun kayan inda suka arce zuwa cikin dazuka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp