Da karfe 3 sauran mintuna 12 na yammacin yau Alhamis, bisa agogon Beijing ne sashen na’urar binciken duniyar wata ta Chang’e-6 da ya tashi daga duniyar wata mai nisa, ya cimma nasarar hadewa da sassa 2 na’urar, a falakin da ke kewayen duniyar wata.
Hukumar kula da harkokin zirga-zirgar sararin samaniya ta kasar ko CNSA ta tabbatar da hakan, inda ta ce, da karfe 3 da mintuna 24 na yammacin yau din, an yi nasarar sanya mazubin dake kunshe da samfuran daga bangaren wata mai nisa irinsu na farko a duniya, cikin sashen na’urar da zai sauko da su doron duniya.
Ana sa ran sashen na’urar da zai dawo doron duniya, zai sauka dauke da samfuran bangaren duniyar wata mai nisa, a yankin Siziwang Banner, na jihar Mongoliya ta Gida mai cin gashin kai, kamar dai yadda aka riga aka tsara. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp