• English
  • Business News
Sunday, May 11, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Yi Shawarwari Karo Na 8 Bisa Manyan Tsare-Tsare Tsakanin Sin Da AU

by CMG Hausa
2 years ago
in Daga Birnin Sin
0
An Yi Shawarwari Karo Na 8 Bisa Manyan Tsare-Tsare Tsakanin Sin Da AU
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Yau Laraba, ministan harkokin wajen kasar Sin Qin Gang, ya gana da shugaban kungiyar AU Moussa Faki Mahamat domin gudanar da shawarwari bisa manyan tsare-tsare karo na takwas tsakanin Sin da AU a hedkwatar kungiyar dake birnin Addis Ababa, fadar mulkin kasar Habasha.

A yayin shawarwarin, Qin Gang ya ce, a ko da yaushe kasar Sin tana dora Afirka a matsayin mai fifiko a harkokin diflomasiyyarta, kuma gado, da ciyar da dangantakar abokantaka tsakanin Sin da Afirka gaba ya zama al’ada mai daraja, kana wani muhimmin tarihi na diflomasiyyar kasar Sin.

  • Da Dumi-dumi: Kotu Ta Kori Mataimakin Kakakin Majalisar Ondo, Ta Maye Gurbinsa

Muna son ci gaba da zama abokan huldar ci gaba tare da Afirka don samun ci gaba tare, da hada karfi don gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga Sin da Afirka a sabon zamani. A cewarsa, kasar Sin ce ke kan gaba wajen tallafawa kungiyar AU ta shiga G20, da goyon bayan inganta wakilci da muryar kasashen Afirka a kwamitin sulhu na MDD, da sauran kungiyoyin kasa da kasa, da kuma kiyaye moriyar kasashe masu tasowa.

A nasa bangaren, Faki ya bayyana cewa, Sin na goyon bayan Afirka, a yayin da jama’ar Afirka ke gwagwarmayar neman ‘yancin kai da ‘yantar da al’umma, da ma kokarin da kasashen Afirka ke yi na hanzarta samun bunkasuwa, da farfadowa, da kuma shiga cikin harkokin kasa da kasa.

Ya kara da cewa, “muna mutunta babban goyon bayan da kasar Sin ke bayarwa ga dunkulewar kasashen Afirka, da cudanya, da gina yankin ciniki cikin ‘yanci, muna kuma fatan yin hadin gwiwa tare da kasar Sin wajen inganta gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga Sin da Afirka a sabon zamani”.

Labarai Masu Nasaba

Kada A Bata Ran Mahaifiya

Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Nuna Gamsuwar Akasarin Jama’a Da Cudanyar Cinikayya Tare Da Sin Fiye Da Amurka

Bayan shawarwarin, bangarorin biyu sun rattaba hannu kan wasu takardun hadin gwiwa, ciki har da yarjejeniyar tattalin arziki, da fasaha kan cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa ta Afirka, tare da halartar bikin kammala ginin hedkwatar cibiyar. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

NIS Za Ta Ƙaddamar Da Cibiyar Bayar Da Sabon Ingantaccen Fasfo A Zariya Da Daura

Next Post

Atiku Ka Yi Wa ‘Yan Nijeriya Bayani Kan Zargin Da Ake Maka Na Cin Hanci Da Matsayin Lafiyarka —Tinubu

Related

Kada A Bata Ran Mahaifiya
Daga Birnin Sin

Kada A Bata Ran Mahaifiya

33 minutes ago
Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Nuna Gamsuwar Akasarin Jama’a Da Cudanyar Cinikayya Tare Da Sin Fiye Da Amurka
Daga Birnin Sin

Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Nuna Gamsuwar Akasarin Jama’a Da Cudanyar Cinikayya Tare Da Sin Fiye Da Amurka

3 hours ago
Wang Yi: Ziyarar Shugaba Xi A Rasha Ta Kara Yaukaka Kawance Da Daidaito Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa
Daga Birnin Sin

Wang Yi: Ziyarar Shugaba Xi A Rasha Ta Kara Yaukaka Kawance Da Daidaito Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa

4 hours ago
Shugaba Xi Zai Halarci Bikin Bude Taron Ministoci Na Dandalin Sin Da CELAC Karo Na 4
Daga Birnin Sin

Shugaba Xi Zai Halarci Bikin Bude Taron Ministoci Na Dandalin Sin Da CELAC Karo Na 4

5 hours ago
Sin Na Fatan India Da Pakistan Za Su Kaucewa Kara Rura Wutar Tashin Hankali
Daga Birnin Sin

Sin Na Fatan India Da Pakistan Za Su Kaucewa Kara Rura Wutar Tashin Hankali

7 hours ago
Tawagar Wanzar Da Zaman Lafiya Ta Farko Ta Sin Ta Dawo Daga Abyei Cikin Nasara
Daga Birnin Sin

Tawagar Wanzar Da Zaman Lafiya Ta Farko Ta Sin Ta Dawo Daga Abyei Cikin Nasara

1 day ago
Next Post
Atiku Ka Yi Wa ‘Yan Nijeriya Bayani Kan Zargin Da Ake Maka Na Cin Hanci Da Matsayin Lafiyarka —Tinubu

Atiku Ka Yi Wa 'Yan Nijeriya Bayani Kan Zargin Da Ake Maka Na Cin Hanci Da Matsayin Lafiyarka —Tinubu

LABARAI MASU NASABA

Kada A Bata Ran Mahaifiya

Kada A Bata Ran Mahaifiya

May 11, 2025
Sojoji Sun Cafke Dillalan Sayar Da Bindigu A Filato

Sojoji Sun Cafke Dillalan Sayar Da Bindigu A Filato

May 11, 2025
Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Nuna Gamsuwar Akasarin Jama’a Da Cudanyar Cinikayya Tare Da Sin Fiye Da Amurka

Kuri’un Jin Ra’ayin Jama’a Na CGTN Sun Nuna Gamsuwar Akasarin Jama’a Da Cudanyar Cinikayya Tare Da Sin Fiye Da Amurka

May 11, 2025
Ɗan Majalisa Ya Tallafawa Mata 400 A Sakkwato

Ɗan Majalisa Ya Tallafawa Mata 400 A Sakkwato

May 11, 2025
Wang Yi: Ziyarar Shugaba Xi A Rasha Ta Kara Yaukaka Kawance Da Daidaito Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa

Wang Yi: Ziyarar Shugaba Xi A Rasha Ta Kara Yaukaka Kawance Da Daidaito Tsakanin Sassan Kasa Da Kasa

May 11, 2025
Shugaba Xi Zai Halarci Bikin Bude Taron Ministoci Na Dandalin Sin Da CELAC Karo Na 4

Shugaba Xi Zai Halarci Bikin Bude Taron Ministoci Na Dandalin Sin Da CELAC Karo Na 4

May 11, 2025
2027: Har Yanzu Ba Mu Saka Ranar Fara Sabunta Katin Zabe Ba — INEC

INEC Na Samun Matsin Lamba Don Kar Ta Yi Wa TNN Rajista — Kakakinta

May 11, 2025
Minista Ya Ƙaddamar Da Yekuwar Wayar da Kan Ɗalibai Kan Kafofin Sadarwa

Minista Ya Ƙaddamar Da Yekuwar Wayar da Kan Ɗalibai Kan Kafofin Sadarwa

May 11, 2025
Uwargidan Jonathan Ta Bayyana Goyon Bayanta Ga Remi Tinubu

Uwargidan Jonathan Ta Bayyana Goyon Bayanta Ga Remi Tinubu

May 11, 2025
Bil’Adama Zai Iya Tabbatar Da Kyakkyawar Makoma Ne Kadai Idan Ya Rike Tarihi A Zuci

Bil’Adama Zai Iya Tabbatar Da Kyakkyawar Makoma Ne Kadai Idan Ya Rike Tarihi A Zuci

May 11, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.