Kwanan nan ne, aka yi shawarwari na matasan sassan kasa da kasa, ciki har da Jamus, da Girka, da Indiya, a wajen taron tattaunawa mai taken “Zurfafa gyare-gyare a Sin a sabon zamaninmu dama ce ga duniya”, inda matasan kwararru, da shahararrun masu amfani da shafunan sada zumunta na intanet, da masu fada-a-ji suka hallara tare da baki daga kasar Sin, don gudanar da tattaunawa kan manyan tsare-tsaren da aka tsara a fannonin da suka shafi ilimi, da kirkire-kirkire da kwararru, a wajen cikakken zama na uku na kwamitin koli karo na 20 na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, gami da yin shawarwari kan damammakin da zamanantarwa irin ta kasar Sin ke haifarwa ga matasan kasa da kasa. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp