Ranar Asabar ta makon da ya gabata aka yi taron kungiyar Baburawa wanda aka saba yi a watan Disamba na kowace shekara na wannan shekarar ma an yi shi ne a Snake Farm wato gonar tsohon shugaban rundunar soja ta kasa Janar Yusuf Brutai (mai ritaya).
Da yake hira da manema labarai Sarkin Baburawa kungiyar wanda kuma har ila yau shine shugaban kungiyar Alhaji Muhammed Baba Maidoki, ya ce makasudin shirya taron wanda ake yi kowace shekara shi ne a rika nunawa da tunatarwa akan al’adun Baburawa, wadanda idan ba a irin hakan ba matasa na yanzu masu tasowa ba za su san su ba.Idan aka yi la’akari kamar yadda yace mutane sun zo daga wurare daban – daban domin su ga yadda al’adunsu suke,ba sai Baburawa ba.
- An Kaddamar Da Shirin The Bond Karo Na Biyar A Kasar Masar
- Dubun Wata Budurwa Da Wasu 5 Ya Cika Bayan Ta Sace Wayoyin Salula 30 Na Matan Aure A Kano
Akwai abubuwa daban- daban wadanda aka yi a ranar wadanda suka hada da nuna irin nau’oin abincin Baburawa wadanda aka kawo domin mutane su gani, bugu da kari kuma an rabawa marayu kayan abinci wanda an dauki matakin ne saboda an san irin matsin rayuwar da ake ciki.
Da aka yima shi tambaya ta yaya suke tara kudaden da suke tafiyar da shi taron sai yace ‘yan kungiyar suna bada gudunmawa ne saboda ayi taron.
An nada mutane tara sarautun gargajiya wadanda kamar yadda Sarkin Baburawa ya ce kafin a yanke shawarar nada su an lura da ganin irin gudunmawar da suke yi wa al’ummar su. Wadanda aka nada sarautun gargajiya sun hada da Alhaji Bukar Bukar (Jakada) Idris Adamu (Shettima) Alhaji Isa Mustafa Biu (Garkuwa) Garka Usman (Turaki) Usman Ibrahim (Gwarzon Baburawa) Injiniya Ibrahim Biu (Wakilin Bayan Dutse) Comrade Nasiru Kabir (Santurakin Baburawa) Abubakar Abdullahi (Dangaladiman Baburawa) Usman Muhammed (Wakilin Shuwari)