An gudanar da taron harkokin waje na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin daga ranar 27 zuwa 28 ga watan Disambar nan a Beijing, inda babban sakataren kwamitin kolin, wanda kuma shi ne shugaban kasa, kana shugaban kwamitin sojan kasar, Xi Jinping ya gabatar da muhimmin jawabi.
Xi ya takaita manyan nasarori da hikimomi masu daraja na harkokin diflomasiyyar kasar Sin masu salon musamman a sabon zamanin da muke ciki, da yin karin haske kan yanayin kasa da kasa da ake ciki, da babban nauyin dake wuyar kasar, a yayin da take tafiyar da harkokin waje, tare kuma da tsara shirye-shiryen ayyukan diflomasiyya na yanzu da kuma na nan gaba.
Firaministan kasar Sin Li Qiang ya shugabanci taron, inda ya jaddada cewa, ya zama dole a gudanar da harkokin diflomasiyya yadda ya kamata, karkashin jagorancin tunanin shugaba Xi a fannin harkokin diflomasiyya, da kuma bullo da bukatu na kara fahimta gami da aiwatar da abubuwan dake cikin jawabin shugaba Xi a zahirance. (Murtala Zhang)