An kira wani taron musamman a Amurka na tattaunawa tsakanin kasa da kasa mai taken “Kirkire-kirkire da budadden kasuwanci, da more damammakin ci gaba” a birnin Washington na Amurka. Babban rukunin gidan rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG da ofishin jakadancin Sin dake Amurka ne suka gabatar da taron cikin hadin gwiwa.
Kusan baki 100 daga Amurka da Sin, ciki har da masana kan harkokin kasa da kasa, malamai, da wakilan matasan Amurka, sun tattauna batutuwa kamar yadda Sin ke amfani da karfin kimiyya da fasaha mai dorago da kai don karfafa kirkire-kirkire a duniya, da fadada budadden kasuwancinta mai zurfi, da more damammaki ga sauran kasashe. Da wannan taron ne aka fara gudanar da jerin tarurrukan tattaunawar kasa da kasa bisa taken taron.
A cikin jawabinsa ta kafar bidiyo, shugaban CMG Shen Haixiong ya bayyana cewa, CMG za ta ci gaba da hadin gwiwa tare da abokan huldarta don kafa dandalin tattaunawa na duniya, da aiwatar da “shawarar ziri daya da hanya daya,” kana da tabbatar da shawarwari 4 a duniya da shugaban kasar Sin ya gabatar, ta yadda Sin za ta samar da moriyar dabarar kasar a bangaren inganta tsarin shugabancin duniya da kuma makomar Sin ta zamanantar da al’ummarta ga kasashen duniya, har kuma ta samar da moriyar karfin kirkire-kirkirenta na zamani ga duk fadin duniya. (Amina Xu)














