An yi taron tattaunawar kasa da kasa mai taken “Sin a lokacin bazara: More damammakin da take samarwa a duniya” a Dakar na Senegal a ran 13 ga watan nan da muke ciki. Mahalarta taron sun tattauna kan damammakin da tsarin zamanatar da al’ummar Sinawa na Sin ke samarwa kasashen Afirka.
Ban da haka kuma, an kira irin wannan taro a Addis Ababa na Habasha a ran 11 ga watan, mahalarta taron sun tattauna kan damammakin da Sin ta samarwa kasashen Afirka a bangaren kirkire-kirkiren kimiya da fasaha da bude kofa da hadin gwiwa.
- Sabon Kawancen Jihohin Arewacin Najeriya Da Kamfanonin Sin Zai Fa’idantar
- Jami’i: Jiragen Saman Kasar Sin Za Su Bunkasa Sashen Sufurin Jiragen Afirka
Bayan ga hakan, an gudanar da wannan taro a birnin London na kasar Birtaniya a ran 17 ga watan nan da muke ciki, taron da babban rukunin gidan rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG ya jagoranta, kana shugaban CMG Shen Haixiong ya halarci taron tare da gabatar da jawabi ta kafar bidiyo.
Cikin jawabin nasa Shen ya ce, yayin tarukan shekara-shekara na NPC da CPPCC na bana, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jadadda wajibcin gaggauta bude kofa mai inganci ga ketare daki-daki, da habaka hadin gwiwar kasa da kasa.
Ya ce ba shakka Sin za ta rika habaka bude kofarta ga ketare sannu a hankali. A cewarsa, a matsayinsa na rukunin yada labarai mafi girma dake shafar mabambantan bangarori a duniya, CMG na fatan amfani da fifikonsa na hada mabambantan hanyoyin watsa labarai waje guda, da mallakar kimiya da fasaha, da kirkire-kirkire a wannan bangare, don more damammakin zamanantar da al’ummar Sinawa da duniya, kana da cin gajiyar damammakin ci gaban kimiya da fasaha, da kirkire-kirkiren kasar Sin, da mu’ammalar al’adu, don taka rawa tare, wajen samun wadatar duniya cikin hadin kai, da kafa kyakkyawar makomar Bil Adam ta bai daya.
A ran 14 ga watan nan, an yi wannan taro a Astana na kasar Kazakhstan. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp