Gwamnatin jihar Bauchi ta sanar da cewa Birgediya Janar Marcus Kokko Yake (mai ritaya) shi ne ya zama Sarkin Sayawa (Gung-Zaar) na farko a sabuwar masarautar Sayawa (Zaar Chiefdom).
Sanarwar na ƙunshe ne ta cikin sanarwar manema labarai da jami’ar watsa labarai ta ma’aikatar kula da harkokin ƙananan hukumomi da Masarautun gargajiya ta jihar Bauchi, Khadija Danladi Hassan Kobi, ta fitar tare da raba wa manema labarai a ranar Litinin.
- Tsohon Gwamnan Jigawa, Lamido Ya Bayyana Aniyar Takarar Shugabancin Jam’iyyar PDP Na Ƙasa
- Kara Bude Kofofin Sin Zai Samar Da Karin Gajiya A Fannin Bunkasar Duniya
A sanarwar ta ce, an gudanar da zaɓen Sarkin a ƙarƙashin dokar kafa masarautar Zaar ta 2025 wanda hakan ya zo bayan sanarwar cewa, dukkanin mai sha’awar zama sarkin ya aike da buƙatar nuna sha’awarsa a rubuce.
Kobi ta ce, an samu buƙata daga wajen mutane bakwai, inda aka tantance su domin fafata neman sa’a, daga baya mutane uku suka janye suka bar mutane huɗu domin fafata neman nasara a zaɓen.
“Bayan gudanar da zaɓen, Birgediya Janar Marcus Kokko Yake (Rtd) shi ne ya yi nasara.
“Za a gabatar da sakamakon nasarar da ya samu wa gwamnan domin amincewar da gabatar wa Gung-Zaar na farko takardar naɗinsa a matsayin Sarkin masarautar Zaar,” sanarwar ta shaida.
Wannan matakin dai na zuwa ne yayin da al’ummar Sayawa ke zanga-zangar adawa da yunƙurin gwamnatin jihar Bauchi ta Bala Muhammad wajen naɗa musu wani a matsayin Sarkin masarautar Sayawa wato (Gung Zaar).
Masu zanga-zangar dai sun bayyana cewa, Air Commodore Ishaku Komo (mai murabus) shi ne wanda suke so tuntuni wanda ya zama jagoransu bisa bin tsarin al’adarsu tun da jimawa. Masu zanga-zangar sun jawo hankalin gwamnatin jihar kan cewa, ta musu abun da suke so ba ƙaƙaba musu wani da ba sa so ba.














