Alhamis din nan ne, aka bude bikin baje kolin litattafai na kasa da kasa karo na 29 a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, taron baje kolin kwanaki hudu da ya hallara kasashe da yankuna 56.
Mahalarta 2,500 ne suka baje kolin litattafai masu taken Sinanci da na kasashen waje sama da dubu 200 a bikin baje kolin na bana, wanda ake gudanarwa ta yanar gizo da kuma a zahiri.
Hukumar kula da harkokin wallafe-wallafe ta kasar Sin, da ma’aikatar kimiyya da fasaha, da gwamnatin birnin Beijing, da kungiyar mawallafa ta kasar Sin, da kungiyar marubuta ta kasar Sin ne suka shirya bikin, inda aka gayyaci kasar Aljeriya a matsayin kasar da aka karrama. (Mai fassarawa: Ibrahim)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp