An kaddamar da babban taron kafofin watsa labarai na kasa da kasa karo na farko mai taken “Kago makomar sana’ar kafofin watsa labarai” a Abu Dhabi, fadar mulkin kasar Hadaddiyar Daular Larabawa a ranar Talata, agogon kasar, inda aka samu halartar wakilai sama da 1000, wadanda suka hada da jami’an gwamnatocin kasashe daban daban, da wakilan kafofin watsa labarai, da ‘yan kasuwa, da masana da sauransu. Babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a takaice, shi ma ya halarci taron a matsayin abokin hadin gwiwa.
Yayin taron, CMG da gidan talabijin na Al Darfrah dake Hadaddiyar Daular Larabawa, sun daddale yarjejeniyar hadin gwiwa kan yadda za a watsa wasan kwaikwayo kimanin 13 na Sinanci da aka fassara zuwa harshen Larabci a gidan talabijin. (Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa)