Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa tana bin masu hakar ma’adanai a Jihar Kaduna bashin naira biliyan 3.5.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Shugaban Sashin Hakar ma’adanai na Shiyyar Arewa Mason Yamma na ma’aikatar, Injiniya Kutama Hosea Ali, a zantawarsa da manema labarai.
- Gwamnatin Tarayya Za Ta Kafa Cibiyar Bunkasa Hakar Ma’adanai
- Kasashen Saudiyya Da Birtaniya Za Su Zuba Jarin Dala Biliyan 20 A Bangaren Hakar Ma’adanai
Ya jaddada cewa, wajibi ne kungiyoyin masu hakar ma’adanai su biya kudade, wanda suke zama a matsayin kudadan sabunta lasisin da aka ba su na hakar ma’adanai.
“Gwamnatin tarayya tana bin masu hakar ma’adanai bashin naira Tiriliyan 3 a fadin kasar nan, wanda daga ciki tana bin masu hakar ma’adanai na Jihar kaduna bashin biliyan 3.5, idan da sun biya kudaden, da gwamnati za ta yi amfani da su wajen aiwatar da ayyukan ci gaba da su. Amma har yanzu ba su biya ba. Kuma biyan kudaden ya zama wajibi a kanku.”
Injiniya Kutama, ya ce biyan irin wadannan kudede zai taimaka wa gwamnati ta samu damar aiwatar da wasu muhimman ayyukan ci gaban a kasa baki daya.
Da yake bayani a kan matsalar tsaro kuma, ya ce idan aka bunkasa harkokin hakar ma’adanai, matsalar tsaro za ta zama tarihi. Yana mai cewa hakar ma’adanai tana samar wa matasa ayyukan yi masu tarin yawa a fadin kasar nan baki daya.
Shugaban ya jawo hankalin masu hakar ma’adanai da su tabbatar da cewa suna yin rajista da kuma sabuntawa da gwamnatin tarayya domin samun damar gudanar da ayyukansu cikin tsari.