Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya soke lasisin wasu kamfanonin masu hada-hadar canjin kudi har guda 4,173.
Babban bankin ya ce bullo da matakin ne a karkashin dokar Bankuna da sauran Cibiyoyin Kudi (BoFIA) ta shekarar 2020.
- Ana Bin Masu Hakar Ma’adanai Bashin Naira Biliyan 3.5 A Jihar Kaduna
- Gwamnatin Kano Ta Kafa Kwamitin Kar-ta-kwana Kan Haramtattun Gine-gine
Wannan na cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Daraktan Sadarwa na CBN, Hakama Sidi Ali, da ya fitar a ranar Juma’a.
CBN ya wallafa jerin sunayen kamfanonin da matakin ya shafa a shafinsa na Intanet a ranar Juma’a.
A cewar CBN, kamfanonin da abin ya shafa sun kasa cika sharudan da suka hada da sabunta lasisi a tsawon lokacin da aka ware musu.
CBN dai ya bijiro da sabbin tanade-tanade da dokoki don daidaita farashin canjin dala, wanda a baya-bayan ta ke neman ta gagari kundila.
Tashin dalar dai ya haifar da tashin farashin kayayyaki a Nijeriya, lamarin da ya ta’azzara kasuwanci da sauran al’amuran yau da kullum.
A gefe guda kuma tattalin arziki ya ci gaba da tabarbarewa, lamarin da ba a taba gani a tarihin kasar ba cikin shekaru 22 da suka gabata.