Al’ummar Nijeriya daga sassa daban-daban na ci gaba da alhinin rasuwar tsohon shugaban majalisar wakilai, Hon. Ghali Umar Na’Abba wanda ya riga mu gidan gaskiya a tsakiyar makon nan.
An gudanar da jana’izarsa a Jihar Kano kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
- Dalilai 20 Da Ke Sa Dalibai Faduwa Jarrabawa (1)
- Majalisar NPC Za Ta Fara Zaman Taron Shekara-shekara A Ranar 5 Ga Watan Maris
Na’Abba ya kasance shi ne shugaban majalisar wakilai na hudu, ya rasu yana da shekaru 65 a duniya bayan ya yi fama da rashin lafiya. Tsohon shugaban majalisar ya kasance dan asalin Jihar Kano wanda aka zabe shi a matsayin dan majalisa mai wakiltar Kano ta tsakiya daga 1999 zuwa 2003.
Ya zama shugaban majalisar ne ‘yan watanni bayan kaddamar da majalisar ta hudu biyo bayan murabus din shugaban majalisar na wancan lokaci, Salisu Buhari daga Jihar Kano, kan badakalar jabun takardun makaranta.
Ya taka muhimmiyar rawar a lokacin da ya zama shugaban majalisar wakilai wajen tabbatar da ‘yancin majalisar a tsakanin bangaren gwamnati, wanda hakan ya haddasa rikici tsakaninsa da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo.
Duk da kasancewarsu ‘ya’yan jam’iyya daya tsakanin Na’Abba da Obasanjo, amma bai hana shi yin gwagwarmaya ba wajen tabbatar da ‘yancin majalisa. Ana ganin cewa rikicinsa da Obasanjo ne ya hana shi ya sake dawowa zauren majalisa.
Kwanan nan ya sauya sheka daga jam’iyyar APC, ya koma babbar jam’iyyar adawa ta PDP.
Tarihinsa ya nuna cewa ya halarci Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a Jihar Kaduna, inda ya karanta kimiyyar siyasa, kuma ya kammala a shekarar 1979.
Kafin rasuwarsa, Na’Abba ya yi fama da rashin lafiya mai tsanani har sai da ta kai an fitar da shi kasar waje domin nema lafiyarsa, kuma ya dawo Nijeriya bayan ya murmure daga cutar da ba a bayyana ba.