Kungiyar ‘Movement for North East Organization Forum’ ta yi kira ga tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, da ya yi hattara da yin katsalandan game da yakin da ake yi da ta’addanci da ‘yan fashi daji.
Shugaban Kungiyar, Alhaji Abdulrahman Buba Kwacham, wanda kuma shi ne Sarkin Fulanin masarautar Mubi a Jihar Adamawa, shi ya yi wannan kira yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja.
Ya lura cewa hukumomin tsaron kasar, karkashin jagorancin Babban Mai Ba Da Shawara Kan Harkokin Tsaro na Kasa (NSA), Malam Nuhu Ribadu, suna aiki tukuru wajen shawo kan matsalolin tsaro.
A cewarsa, ci gaban da ake samu wajen dawo da zaman lafiya a sassa daban-daban na kasar ya cancanci yabo maimakon suka.
Kwacham ya kara da cewa jami’an tsaro sun samu gagarumar nasara wajen kwato yankuna da a baya ‘yan bindiga suka mamaye, tare da rage yawaitar satar mutane, satar shanu da sauran ayyukan laifi.
Ya yaba wa Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaro na Kasa (NSA) bisa nasarorin da aka samu kwanan nan, ciki har da cafke wasu shugabannin ‘yan bindiga a Jihar Neja.
“Ya kamata kowa ya dauki tsaro a matsayin alhakin da ya rataya a wuyansa, kuma ya guji siyasantar da batun,” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp