Da safiyar yau Litinin ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gudanar da taron manema labarai, bisa taken “Cimma burikan da aka tsara domin neman bunkasa tattalin arziki da zaman takewar al’umma a tsakanin shekarar 2021 zuwa shekarar 2025”.
A yayin taron, jami’in babbar hukumar buga haraji ta kasar Sin ya bayyana cewa, tun daga shekarar 2021 ya zuwa yanzu, tattalin arzikin kasar Sin ya bunkasa bisa shirin da aka tsara, kana, bisa hasashen da aka yi. Sakamakon haka, jimillar haraji da kudaden da hukumomin buga haraji sun karba ta zarce kudin Sin Yuan tiriliyan 155, adadin da ya kai kaso 80 bisa dari na yawan kudaden shiga na kasar Sin. Cikin adadin, kudin haraji zai kai sama da Yuan tiriliyan 85, adadin da ya karu da Yuan tiriliyan 13, idan aka kwatanta da adadin kudin haraji da aka samu a tsakanin shekarar 2015 zuwa shekarar 2020. Lamarin da ya ba da tabbaci ga bunkasar tattalin arziki da zaman takewar al’umma.
A sa’i daya kuma, jami’in ya ce, tun daga shekarar 2021, ya zuwa yanzu, jerin manufofin da aka samar a fannin rage haraji, da kudaden da hukumomin buga haraji suka karba, ya nuna goyon baya ga aikin raya tattalin arziki da kyautata zaman takewar al’umma. Hasashen da aka yi ya kuma nuna cewa, tsakanin shekarar 2021 da ta 2025, yawan haraji da kudaden da hukumomin buga haraji suka rage, ya kai kudin Sin Yuan tiriliyan 10.5, kana, yawan harajin da aka mayar kan kayayyakin fitarwa ya kai Yuan tiriliyan 9. (Mai Fassara: Maryam Yang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp