• English
  • Business News
Monday, October 20, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ana Ci Gaba Da Samun Rudani Yayin Da INEC Ta Jinkirta Rajistar Sabbin Jam’iyyu

by Yusuf Shuaibu and Sulaiman
5 months ago
Inec

Ana ci gaba da samun rudani yayin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta jirkinta yin rajistar kungiyoyi siyasa fiye da 104 da ke neman zama jam’iyyun siyasa kafin zaben 2027.

Wannan na zuwa ne bayan korafe-korafen daga ‘yan siyasa, kwararru a fannin shari’a, da kungiyoyin fararen hula game da jinkirin hukumar na rashin bayyana gaskiya, da zargin yin katsalandan a cikin harkokin siyasa.

  • INEC Ta Samar Da Sashen Ƙirƙirarriyar Basira Domin Inganta Harkokin Zaɓe 
  • Kashi 70 Na Fursunonin Nijeriya Ba A Yanke Musu Hukunci Ba

Bukatar neman rajistar sabbin jam’iyyu sun karu ne tun bayan kammala zabukan 2023, inda wasu kungiyoyi kamar kungiyar hadakan ‘yan adawa ta kasa suka fito fili suka kalubalanci yunkurin sake zaben Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a karkashin sabuwar jam’iyyar siyasa, wanda aka ba ta suna na dan lokaci a matsayin hadakan dimokuradiyya (ADA).

Manyan ‘yan adawa, ciki har da Kwamared Salihu Lukman, tsohon jigo na APC, sun zargi cewa INEC na jinkirta tsarin rajistar da gangan ta hanyar kin amincewa da neman bukatar, wanda lamarin ya saba wa sashe na 75 na dokar zabe ta 2022.

“Fiye da kungiyoyi 70 suka gabatar da takardun neman izini zuwa INEC. Amma INEC tana jan kafa kan lamarin.,” in ji Lukman a cikin wani tattaunwa da shi.

LABARAI MASU NASABA

An Shiga Ruɗani A Borno Bayan Budurwa Ta Kashe Kanta Saboda Auren Dole

Ƙungiyar Ƙwadago Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Ta Sasanta Da ASUU

Wani Lauya Okere Kingdom Nnamdi, wanda ya gabatar da takardu don samun rajistar Jam’iyyar Mutanen Kasa (PPP) a ranar 28 ga Maris, 2025, ya ce bayan wata daya sai INEC ta bayyana cewa ba ta bude adireshin fara yin rajistar sabbin jam’iyyun siyasa.

Jami’an INEC da suka yi magana kan lamarin, sun musanta zarge-zargen. Sun bayyana cewa duk da cewa an karbi bukatar yin rajista har guda 104, ana ci gaba da gudanar da bincike, sannan kuma tsarin zai fara gudana nan ba da dadewa ba ta hanyar sadarwaar zamani don inganta gaskiya da ingancin aiki.

“Hukumar ta amsa wa masu nema. Ba daidai ba ne a zargi INEC da jinkirin amsa bukatun yin sabbin rajistar. Za a bude Shafin intanet dazarar an kammala duk wani aikace-aikacen da suka cika ka’ida,” in ji wani babban jami’in hukuman.

Mai magana da yawun INEC, Rotimi Oyekanmi, ya sake jaddada cewa kungiyoyin siyasa dole ne su bi doka da oda na tsarin mulkin kasa kafin a yi musu rajista.

“Dole ne INEC ta tabbatar da cewa an bin doka. An bayyana ka’idojin, kuma har idan mai nema bai cika su ba, to ba za a iya masa rajistar ba har sai ya cika,” in ji shi.

Wani mai sharhi kan harkokin shari’a ya bayyana cewa jinkirin aiwatar da rajistar na iya kawo cikas ga shirin zabe, musamman ganin cewa ana sa ran fara zaben fid da gwani na jam’iyya a tsakiyar 2026.

Tsohon shugaban kungiyar siyasa ta kasa da kasa, Farfesa Adele Jinadu ya ce, “Idan masu nema sun bi ka’idojin kundin tsarin mulki da na zabe, babu wata kuntatawa ga rajistar jam’iyya a karkashin tsarin jam’iyyu masu yawa.”

Dakta Dauda Garuba na cibiyar ci gaban dimokiradiyya (CDD) ya kara da cewa, “Idan aka bai wa jam’iyyu damar gudanar da aikinsu cikin ‘yanci da zaman kansu, da yawa daga cikin kalubalen da muke fuskanta a yau ba za su taso ba.”

A ranar 6 ga Maris 2025 ne, majalisar wakilai ta amince da karatu na biyu kan kudirin dokar da ke neman canza rajistar da tsarin kula da jam’iyyun siyasa daga INEC zuwa wani sabon hukuma mai zaman kanta.

Kudirin hadin gwiwa tsakanin shugaban majalisan, Abbas Tajudeen da dan majalisa, Marcus Onobun, wannan kudurin na bayar da shawarar kafa kotun kula da takaddama tsakanin jam’iyyu don warware rikici cikin gida da rikice-rikicen tsakanin jam’iyyun.

An tura kudirin zuwa kwamitocin da ke kula da al’amuran zabe da kuma jam’iyyun siyasa don kara dubawa.

Duk da karuwar kiraye-kiraye na shiga harkokin siyasa, masu nazari da yawa na ganin cewa lokaci na kurewa ga sabbin jam’iyyun wajrn yi musu rajista yadda ya kamata da kuma shirya su kafin zaben 2027.

Shugaban jam’iyyar AA, Barrister Kenneth Udeze ya yi gargadin cewa, “Bai kamata a yi rajistar kowace jam’iyya ba kasa da watanni 12 kafin zabe. Bisa fatan gudanar da zaben fid da gwani na jam’iyyun a tsakiyar 2026, lokaci na kara kuantowa.

A halin yanzu, Nijeriya na da jam’iyyun siyasa 19 da aka tabbatar da rajistarsu, daga cikin 91 bayan INEC ta cire rajistar jam’iyya 74 a shekarar 2020 bisa ga rashin kwazonsu. Jam’iyyun da suka rage sun hada da APC, PDP, LP, NNPP, SDP, ADC, da sauransu.

Irin su, jam’iyyar matasa (YP) da jam’iyyar Boot (BP) sun sake samun rajista ta hanyar hukuncin kotu, wanda ya nuna yiwuwar kalubale na shari’a nan gaba idan INEC ta ci gaba da jinkirin rajista.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Shiga Ruɗani A Borno Bayan Budurwa Ta Kashe Kanta Saboda Auren Dole
Labarai

An Shiga Ruɗani A Borno Bayan Budurwa Ta Kashe Kanta Saboda Auren Dole

October 20, 2025
Ƙungiyar Ƙwadago Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Ta Sasanta Da ASUU
Labarai

Ƙungiyar Ƙwadago Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Ta Sasanta Da ASUU

October 20, 2025
Mutane 3,433 Sun Rasa Rayukansu A Haɗurra 6,858 A Cikin Watanni Tara
Manyan Labarai

Mutane 3,433 Sun Rasa Rayukansu A Haɗurra 6,858 A Cikin Watanni Tara

October 20, 2025
Next Post
Tottenham Ta Raba Gari Da Kocinta Ange Postecoglu

Tottenham Ta Raba Gari Da Kocinta Ange Postecoglu

LABARAI MASU NASABA

Matsayar Kasar Sin A Bayyane Take Dangane Da Batutuwan Cinikayya Da Tsagin Amurka

Matsayar Kasar Sin A Bayyane Take Dangane Da Batutuwan Cinikayya Da Tsagin Amurka

October 20, 2025
An Shiga Ruɗani A Borno Bayan Budurwa Ta Kashe Kanta Saboda Auren Dole

An Shiga Ruɗani A Borno Bayan Budurwa Ta Kashe Kanta Saboda Auren Dole

October 20, 2025
Sin Ta Kara Wasu Wurare 22 Cikin Yankunan Dausayi Masu Matukar Muhimmanci A Kasar

Sin Ta Kara Wasu Wurare 22 Cikin Yankunan Dausayi Masu Matukar Muhimmanci A Kasar

October 20, 2025
Tinubu Ya Taya Kwankwaso Murnar Ranar Haihuwa, Ya Jaddada Abotarsu

Tinubu Ya Taya Kwankwaso Murnar Ranar Haihuwa, Ya Jaddada Abotarsu

October 20, 2025
Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta Tsakanin Pakistan Da Afghanistan

Sin Ta Yi Maraba Da Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta Tsakanin Pakistan Da Afghanistan

October 20, 2025
Ƙungiyar Ƙwadago Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Ta Sasanta Da ASUU

Ƙungiyar Ƙwadago Ta Bai Wa Gwamnatin Tarayya Wa’adin Mako 4 Ta Sasanta Da ASUU

October 20, 2025
Gina Kasar Sin Ta Dijital Na Kara Gaba Zuwa Sabon Matakin Amfani Da Basira

Gina Kasar Sin Ta Dijital Na Kara Gaba Zuwa Sabon Matakin Amfani Da Basira

October 20, 2025
Mutane 3,433 Sun Rasa Rayukansu A Haɗurra 6,858 A Cikin Watanni Tara

Mutane 3,433 Sun Rasa Rayukansu A Haɗurra 6,858 A Cikin Watanni Tara

October 20, 2025
An Gudanar Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Tsakiyar JKS Na 20 A Beijing

An Gudanar Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Tsakiyar JKS Na 20 A Beijing

October 20, 2025
Gwamna Lawal Ya Jaddada Muhimmancin Haɗin Kai Wajen Yaƙi Da Ƙalubalen Tsaro

Gwamna Lawal Ya Jaddada Muhimmancin Haɗin Kai Wajen Yaƙi Da Ƙalubalen Tsaro

October 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.