Al’umar jihar Sakkwato na cikin zullumi da fargabar yadda hukuncin kotun daukaka kara zai kasance a yau Litinin a tsakanin Gwamna Ahmed Aliyu na jam’iyyar APC da Sa’idu Umar na jam’iyyar PDP.
A sanarwar da kotun daukaka kara ta fitar a daren jiya a Abuja ta bayyana cewar za ta raba gardamar shari’ar zaben Gwamnan na ranar 18 ga watan Maris a yau Litinin da misalin karfe 03: 00 na rana.
- Kotun Zaben Gwamnan Sokoto Ta Kori Karar PDP Ta Tabbatar Da Nasarar Zaben Aliyu
- Shari’un Zabe: A Kauce Wa Tarzoma Duk Yadda Ta Kaya
- Gwamnonin Da Ke Kan Tsini A Shari’ar Zabe
LEADERSHIP Hausa ta rawaito cewa, alkalai uku na kotun sauraren karar zabe a karkashin jagorancin Mai Shari’a Haruna Mshelia a ranar 30 ga Satumba sun sa kafa sun yi watsi da karar PDP da dan takararta bisa ga rashin gamsassun hujjoji.
Kotun ta ce masu kara sun kasa tabbatar da korafe- korafen su kan rashin cancantar Aliyu da mataimakinsa Idris Gobir na tsayawa takara da gaza gamsar da kotu da hujjojin takardun bogi, sabawa dokokin zabe da tayar da hankali a lokacin zabe. Haka ma kotun ta ce batun bambancin sunaye lamari ne da kotun koli ta riga ta kawo karshen matsalar.
Dukkanin magoya bayan jam’iyyun biyu dai suna cikin zullumi musamman kasancewar ba a san yadda sakamakon hukuncin kotun daukaka karar zai kasance A tsakanin APC da PDP ba.