Yayin da ake dakon kammaluwar ginin hedkwatar cibiyar kandagarki da dakile yaduwar cututtuka ta Afrika CDC da kasar Sin ke daukar nauyi, hazikan injiniyoyin Sin da Afrika sun dukufa ba tare da la’akari da zafin rana na tsakiyar watan Disamba ba, a karkarar birnin Addis Ababa na Habasha, domin kammala aikin a kan lokaci.Â
Nasarar ginin na zamani dake daukar saiti, kuma yake gab da kammaluwa, na samun yabo sosai, lamarin da ya kara fatan da ake da shi na ganin sauyi a tsarin kiwon lafiyar al’ummar Afrika.
Monique Nsanzabaganwa, mataimakiyar shugaban hukumar AU, ta shaidawa Xinhua cewa, idan aka kammala aikin, zai ba cibiyar CDC ta AU, damar kara taka rawa wajen tsarawa da aiwatar da ayyukan gaggawa a fannin kiwon lafiyar al’umma.
A nasa bangare, mukaddashin daraktan cibiyar, Ahemd Ogwell, ya ce duk da kasancewarta mai kananan shekaru, cibiyar da aka kaddamar a Junairun 2017, ta yi kokarin tunkarar cututtuka daban daban da suka barke yadda ya kamata, kamar sake bullar cutar Ebola da annobar COVID-19.
Ya ce yayin da annobar COVID-19 ta barke, nahiyar Afrika da Sin sun yi kokarin tabbatar da gudanar bayanai yadda ya kamata a tsakaninsu.
Ya ce sun yi aiki sosai wajen samun kayayyakin gwaji a farkon barkewar annobar, kuma sun bunkasa kwarewarsu a gida. Haka zalika, takwarorinsu na kasar Sin, sun taimaka a lokacin da al’amura suka yi tsanani ta fuskar tunkarar cutar a nahiyar. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha daga CMG Hausa)