A farkon lokacin baraza na bana, an fara gaggauta raya manyan ayyukan ban ruwa a sassan kasar Sin, wadanda suka samu nasarori da dama.
Ya zuwa ranar 5 ga wannan wata, yawan ruwan da aka janyo daga kudu zuwa arewacin kasar Sin a matakin farko na aikin da aka gudanar a yankin gabashi da tsakiyar kasar Sin, ya kai kyubik mita biliyan 60, inda yawan ruwan ya kai kwatankwacin wanda ake samu a Rawayen Kogi fiye da shekara daya.
A matsayin wani tsari na magance ambaliyar ruwa a yankin kogin Huai, mataki na biyu na aikin shigar da ruwan kogin Huai zuwa teku, zai fadada hanyoyin kai ruwan kogin zuwa teku.
Ban da wannan kuma, ana gaggauta aikin inganta ruwan sha a wasu kauyukan kasar Sin, inda ake kokarin cimma burin ganin kashi 88 cikin dari na kauyukan kasar Sin sun samu ruwan fanfo a karshen shekarar bana. (Zainab)