Wata tsohowar giwa mai suna Dida da ke da shekara 65 a duniya ta mutu a gandun dajin Tsavo da ke kasar Kenya wacce ta kasance giwa mai tarihi da har ta zama Sarauniyar Giwaye na kasar.
Hukumar kula da namun dajin kasar ta ce giwar ta mutu ne sakamakon yawan shekaru.
Marigayir giwar ta sha tsallake kalubale da dama a kasar kamar farin da kasar ke fuskanta.
A wasu jerin sakonni da ma’aikatan gandun dajin kasar suka yi ta wallafawa a shafukansu na Tuwita, sun bayyana kaduwa da alhininsu bayan mutuwar ‘sarauniyar Giwayen’.
Gandun dajin ya bayyana Dida a matsayin giwar da gandun dajin ba zai taba mantawa da ita ba.
Haka kuma an bayar da rahoton mutuwar wasu giwayen biyu a gandun dajin Imenti na kasar.
A ‘yan watannin baya-bayan nan dai ana samun karuwar yawan mace-macen dabbobin dawa, lamarin da ya haddasa mutuwar giwaye sama da 100 a gandun dazukan kasar da daban-daban, kamar yadda gidauniyar kula da namun daji ta Afirka ta bayyana.
Masu kula da gandun dajin na ganin hakan a matsayin wani koma baya ga fannin tattalin arzikin kasar.