An bayyana zaben shugaban Zimbabwe Emmerson Mnangagwa a matsayin shugaban kungiyar raya kudancin Afrika ta SADC, a matsayin abun da zai taimaka wajen bunkasa hadin kan Sin da kasashen kungiyar.
Munetsi Madakufamba, babban daraktan cibiyar bincike da adana bayanai ta yankin kudancin Afrika (SARDC) kuma abokiyar huldar SADC, wadda ke da mazauni a Harare, babban birnin Zimbabwe, ya shaidawa manema labarai cewa, suna da kyakkyawan fata ga dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrka (FOCAC), ciki har da kara daukaka hadin kai ta kowace fuska, tsakanin Sin da Zimbabwe da kuma Sin da SADC.
Munetsi Madakufamba ya bayyana haka ne ranar Talata, yayin wani taron karawa juna sani na rabin yini da aka yi a Harare, domin tattauna hanyoyin karfafa dangantaka tsakanin Sin da kungiyar SADC gabanin taron dandalin FOCAC da za a yi a farkon wata mai kamawa.
Cibiyar nazarin dangantakar Sin da Afrika a yankin kudancin Afrika ta kungiyar SARDC da cibiyar nazarin nahiyar Afrika ta jami’ar Peking na kasar Sin ne suka shirya taron. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp