Ya zuwa yanzu ana zaman jiran fara karbar sakamakon zaben gwamnan Jihar Bauchi da aka gudanar a ranar Asabar.
Wakilinmu da ya kasance a ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ke Bauchi ya labarto cewa har zuwa karfe 11:33am na safiyar nan ba a fara amsar sakamakon zaben daga kananan hukumomi a hukumance ba.
- PDP Ta Kwace Kujerar Kakakin Majalisar Dokokin Yobe Da Tazarar Kuri’u 182
- Da Dumi-Dumi: Mace Ta Kayar Da Kakakin Majalisar Filato Da Tazara Mai Yawa
Bisa tsari, jami’an da suka tattaro sakamakon zaben daga kananan hukumomin za su zo gaban babban jami’in tattara sakamakon zaben gwamnan tare da gabatarwa hadi da sanya idon wakilan jam’iyyu da masu sa ido da jami’an tsaro.
Sai dai har zuwa lokacin aiko da rahoton nan ba a fara amsar sakamakon zaben ba duk da wakilinmu ya ce akwai kananan hukumomi 7 da aka ce sun riga sun kammala tattara sakamakon har ma sun kawo suna zaman jiran a amsa.
Kananan hukumomin da suke jiran a amshi sakamakon zaben su zuwa yanzu sun hada da karamar hukumar Kirfi, Warji, Jama’are, Bogoro, Giade, Itas Gadau da kuma Gamawa.
Ana dai zaman jira zuwa aiko da rahoton nan. Sai dai alamu na nuni da cewa za a iya fara amsa a kowani lokaci.