Mataimakin kwamishinan ‘yan sandan da aka dakatar, Abba Kyari, na sake fuskantar wata sabuwar shari’a yayin da gwamnatin tarayya ta sake bankado wasu kadarori da take zarginsa da su a Abuja da Maiduguri a jihar Borno.
LEADERSHIP ta samo cewa, gwamnatin tarayya ta gano wasu kadarori 14 da suka hada da wajen kasuwanci, jerin gidajen zama, filin wasan Polo, filaye da filayen noma wadanda tsohon kwamandan IRT ya ki bayyanawa.
Haka kuma an gano sama da Naira miliyan 207 da kuma Yuro 17,598 a asusun ajiyarsa na banki.
Daraktan shigar da kara da shari’a Joseph Sunday ne ya bayyana hakan, inda ya kara da cewa an kara gurfanar da Kyari a gaban kotu a ranar 30 ga Agusta, 2022.
Har ila yau, shugaban masu gabatar da kara da kuma lauyoyi na hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, Stephen Kashawa, ya tabbatar da hakan a wata takardar amincewa da tuhume-tuhumen da wani jami’in shari’a ya mika masa.