Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Alhaji Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya yi kira da a gaggauta cafkewa da gurfanar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar kan zargin baya-bayan da ake yi masa na hada kai da tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo wajen wawushe dukiyar al’umma a lokacin da suke kan mulki.
LEADERSHIP ta yi tilawar cewa, wani mutum Michael Achimugu, da ya kira kansa tsohon hadimin Atiku, ya sake wani faifan bidiyo inda ke bada cikakken bayanin yadda ya zargi Atiku da yin amfani da kamfanonin da ake kira ‘Special Purpose Vehicles’ (SPVs) wajen amsar cin hanci tare da karkatar da dukiyar jama’a a lokacin da yake matsayin mataimakin shugaban kasa a karkashin mulkin Obasanjo.
A cikin bidiyon da ya yadu a kafafen sadarwar zamani, Achimugu ya gargadi ‘yan Nijeriya da kada su zabi Atiku bisa zarge-zargen rashawa. Ya kuma yada sautin murya na muhawararsa da Atiku da wasu shaidu da duk yake son tabbatar wa jama’a zargin da yake yi.
Da ya ke bayyana ra’ayinsa kan bayanin na Achimugu a ranar Litinin a Abuja ta bakin kwamitin yakin zaben APC a wani taron manema labarai da suka kira, Tinubu ya hakikance kan cewar a kama Atiku kawai, ya ce, tsohon mataimakin shugaban kasan bai cancanci samun kariya kawai don yana takarar shugaban kasa ba.
Babban mai magana da yawun kwamitin yakin zaben Tinubu, Festus Keyamo (SAN) ya ce, dole ne Atiku ya nemi gafara kuma ya yi watsi da muradinsa na neman Shugaban kasa.
Keyamo, ya kara da cewa, bai kamata jami’an tsaro su yi wata-wata wajen ganin cafke Atiku, ya ce kada su tsaya tunanin don yana takarar ba za a tuhumeshi ba.
Keyamo na cewa, “Sama da mako guda ke nan, ‘yan Nijeriya sun tsunduma cikin mamaki kan bayanin da Mr. Michael Achimugu ya fitar kan hujjojin da ya fitar da ke zarginsa da sama da fadi da dukiyar al’umma ta hanyar amfani da “Special Purpose Vehicles” (SPVs).
“Wadannan kamfanonin SPVs da Atiku ya musu rijista lokacin da ya zama mataimakin shugaban kasa tare da amincewar (Shugaban kasa Olusegun Obasanjo) tare da yin amfani da abokansa da makusantansa a matsayin masu hannun jari da daraktocin kamfanin. Kawai sun yi hakan ne da manufar karkatar da duniyar gwamnati ta hanyar amfani da wadannan kamfanonin.
“Dukkaninmu za mu iya tunawa lokacin da suke mulki, Shugaban kasa Olusegun Obasanjo da Atiku Abubakar sun gina jami’ar Bells da jami’ar American University bi da bi. Yanzu, mun fahimci inda kudin ya fito.
“Mun samu kwararan shaidu daga wajen Mr. Michael Achimugu, kafin mu yi kiran a kama Atiku.”