Wata kungiya mai suna ‘Gamayyar matasan Gaya’, a karshen makon nan, ta bayyana yadda ta bankado wani dan majalisar wakilai mai wakiltar Gaya/Ajinji/ Albasu a jam’iyyar APC, Abdullahi Mahmud Gaya, yake amfani da takardun shaidar karatu na bogi.
Jaridar Daily Times ta rawaito cewa, Kungiyar ta bayyana haka a cikin wata sanarwa da suka rabawa manema labarai, tare da sa hannun ‘Yan kungiyar baki-daya.
- ‘Yansanda Sun Cafke Mutane 5 Da Ake Zargi Da Hannu A Kisan Dan Sanata Gaya
- Zaben APC: Yanzu Haka ‘Yan Takara Uku Sun Janye Wa Osinbajo —Sanata Gaya
Sanarwar ta ce: “A wani lamari mai ban mamaki da al’ajabi, an gano wani dan siyasa a Kano da yin amfani da takardun karatu na bogi.”
“Dan siyasar wanda ya rike mukami a gwamnatin jiha, yanzu kuma dan majalisa ne mai ci mai wakiltar mazabar Gaya, Ajingi da Albasu, ya yi ikirarin cewa ya samu takardar shaidar kammala karatun ‘Advance Diploma’ a Jami’ar Abuja.
Kungiyar ta yi ikirarin cewa bayan binciken da aka yi an gano cewa ba a bi doka ba wajen kammala karatun kuma takardun shaidar karatun sun nuna yadda dan majalisar ya fadi wani kwas bai gyara jarrabawar ba, amma ba’a san dalilin da ya sa hukumar jami’ar ta kawar da kai ta bayar da sakamakon ba tare da bin tsarin da ya dace ba a shekarar 2001.
Kungiyar ta ce wasu gungun ‘yan jarida ne da suka gudanar da bincike kan dan siyasar suka gano hakan, inda suka tuntubi jami’ar da tambayoyi domin tabbatar da sahihancin takardar da ya haifar da rudani.
Wakilin LEADERSHIP HAUSA ya tuntubi mai taimaka wa dan majalisar a bangaren yada labarai, Malam Abba Dukawa, ya ce sam maganar zargin da ake wa dan majalisar ba shi da tushe bare makama, kuma su bama su san da wata kungiya mai wannan sunan ba.
Sai dai kuma Jaridar ta Daily Times ta ci gaba da cewa binchiken na duba sahihancin takardun an gano hakan ne biyo bayan gano takardun da dan majalisar ya mika wa hukumar INEC na shaidar kammala makarantar firamare wacce ke dauke da sunan wani daban da nasa sunan, daga takardun da ya mika a fom dinsa mai suna CF001 wadda ita ce takardar rantsuwa da shaida wadda ita Hukumar zaben take amfani da ita wajen tantance ‘yan takara, an gano cewa a nan ma ya mika takardar shaidar kammala karatun firamare ta bogi mai dauke da sunan Abdullahi Mohd yayin da sauran takardunsa ke dauke da sunan Mahmud Abdullahi Gaya.
Kungiyar ta ce bata san dalilin da yasa ya cire takardar shaidar ‘Advance Difloma’ daga wannan fom din na CF001 da ya cike domin yin takara a zaben 2023 ba, wadda ya saka ta yayin da yayi takara a zaben 2019.
Kungiyar ta ce mutane da yawa sun nuna shakku kan aminncewar INEC idan har za a iya amfani da wannan kwamachala akan idonta, wannan kuma ya kawo ayar tambaya game ingancin ilmin da dan siyasar ya yi a baya.
Idan za a iya tunawa an taba samun makamancin irin wannan zargin kan, Salisu Buhari, wanda shi ma ya ahiga zabe ya kuma yi nasara da jabun takardun karatu kamar yadda zargin ya nuna a wancan lokacin kuma lokacin da ya nemi wakilcin majalisar tarayya a karamar hukumar Nasarawa ta Jihar Kano.