ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sharhi:Yadda Amurka Ke Wasa Da Hankalin Al’umma

by CMG Hausa
4 years ago
Amurka

A kwanakin baya, yadda wasu manyan abubuwan da suka faru a kasar Amurka sun jawo hankalin kasa da kasa. Na farko shi ne yadda wani jirgin kasa ya kauce daga layin dogon da yake bi a jihar Ohio ta kasar, na biyu shi ne yadda ake zargin gwamnatin Biden da tsara shirin lalata bututun iskar gas da ke tsakanin Rasha da Turai, na uku kuma shi ne yadda kasar Amurka ta harbo wani balan-balan na kasar Sin da makami mai linzami, sai dai yadda gwamnatin kasar Amurka ke mayar da martani ga batutuwan da ma yadda kafofin watsa labarai na kasar ke ba da rahotanni suna ba jama’a mamaki.

Jirgin kasan da ya kauce daga kan layin dogo yana dauke da sinadarai masu guba, lamarin da ya gurbata muhallin wurin sakamakon yadda sashen kula da al’amuran gaggawa na wurin ya daidaita hadarin, inda mazauna wurin suka fara ciwon kai da nuna sauran alamu na rashin lafiya, baya ga kuma dimbin kifayen da aka gano sun mutu a cikin kogunan wurin.

A sa’i daya kuma, sanannen dan jarida na kasar Seymour Hersh ya fitar da wani rahoton bincike, inda ya zargi gwamnatin Joe Biden da lalata bututun jigilar iskar gas na Nord Stream, don neman cimma moriyar kanta. Wadannan manyan abubuwa ne da suka shafi rayuwar al’ummar kasar Amurka da ma sunan kasar, amma abin mamaki shi ne, gwamnatin Amurka da kuma manyan kafofin yada labarai na kasar duk sun yi shiru, a yayin da kuma suke ta rura wutar batun wai “balan-balan na kasar Sin”.

ADVERTISEMENT

Shin me ya faru ga gwamnatin Amurka da kafofin watsa labarai na kasar?

Me ya sa suke iya ganin balan balan da ta ratsa sararin samaniyar kasar bisa kuskure wanda ke da tsayin mita 18,000 daga doron duniyarmu, amma sun kasa ganin gurbatacciyar hayakin da ke saman jihar Ohio? Me ya sa suke ta rura wutar zancen barazana daga sauran kasashe, amma kuma suka kawar da ido daga hakikanin abin da ke barazana ga lafiyar al’ummar kasar?

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Me ya sa a farkon fashewar bututun Nord Stream, suka daga murya suka ce dole a hukunta wadanda suka aikata laifin, amma kuma suka yi shiru bayan da Seymour Hersh ya fitar da rahotonsa?

A game da wannan, mai fashin baki kan harkokin siyasar kasar Amurka Alex Krainer ya yi nuni da cewa, lokacin da Amurka ke kokarin rura wutar batun “balan-balan na kasar Sin, a daidai lokacin ne da jirgin kasan ya kauce daga kan layin dogo da kuma Seymour Hersh ya fitar da rahotonsa, kuma dalilin da ya sa ta yi hakan shi ne don kawar da hankalin al’umma daga hakikanin matsalolin da suke fuskanta.

To, ashe wasa da hankalin al’umma ke nan Amurka ke yi. (Mai zane:Mustapha Bulama)

Amurka
CMG Hausa
+ postsBio
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Shugabannin Kasashen Duniya Sun Yi Wa Sin Fatan Alheri A Sabuwar Shekara
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    San Francisco sabon mafarin hadin gwiwar Sin da Amurka ne
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Xi Ya Halarci Kwaya-Kwaryan Taron Shugabannin Mambobin APEC
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Shugaban Kasar Sin Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Jagororin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC

MASU ALAKA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
Daga Birnin Sin

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
Daga Birnin Sin

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Daga Birnin Sin

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Next Post
Jami’in MDD: Fasahohin Sin Za Su Taimaka Wa Afirka Tinkarar Matsalar Sauyin Yanayi

Jami’in MDD: Fasahohin Sin Za Su Taimaka Wa Afirka Tinkarar Matsalar Sauyin Yanayi

LABARAI MASU NASABA

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

’Yan Takarar ADC A Arewa Maso Yamma Sun Yi Alƙawarin Biyan N110,000 A Matsayin Mafi Ƙarancin Albashi

September 9, 2026
Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa

Na Sayar Da ’Ya’yana, Na Sace Wasu 19 – Wata Da Ake Zargi Da Safarar Yara

September 9, 2026
Iran Ta Musanta Ikirarin Trump Tare Da Zafafa Hare-hare Kan Isra’ila

Hormuz: Iran Ta Kai Muggan Hare-hare Kan Sansanin Amurka A Jordan

September 9, 2026
ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

ASUU Ta Yi Barazanar Yajin Aiki A Jami’ar Jihar Sokoto

September 9, 2026
Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.