A halin yanzu bayani ya nuna cewa, ba a bayar da sakamakon zaben mazabar kujerar majalisar dattawa na Kebbi ta tsakiya ba saboda rashin samun sakamakon zabe daga mazaba daya daga cikin sakamakon kananan hukumomi 8 na yankin, bayani ya nuna cewa wai jami’in zaben mazabar Marafa wanda ita kadai ake jira ya yi batan dabo.
Wannan tsaikon ya tayar wa da al’ummar yankin hankali inda suke ganin kamar wata kutunguila ce ake yi na murde zaben, musamman ganin ya zuwa yanzu tazarar da ke tsakanin jam’iyyar PDP da jam’iyya mai ci ta APC ya zarce 50,000 abin kuma da ake jira daga mazabar Mafara bai zarce kuri’a 6,000 ba.
A jawabinsa ga manema labarai, jami’in watsa labarai na jami’iyyar PDP, kuma tsohon shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kebbi, Alhaji Sani Dododo, ya yi kira ga shugaban zabe Mahmood Yakubu da dukkan masu ruwa da tsaki, musamman Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da su sa baki don ganin an bayyana sakamamon zaben da aka yi don kaucewa tashe-tashen hankula.
Ya kara da cewa, “An kasa fitar da sakamakon zaben kananan hukumomi 7 daga cikin kananan hukumomi 8 dake cikin mazabar Kebbi ta tsakiya, kuma jam’iyar PDP tana da rata daga dukkan kananan hukumomin da aka bayyana sakamakonsu na fiye da kuri’a 50,000, a bayanan da muke samu saboda haka, bamu san dalilin da za a kawo wannan lokaci ba a sanar da sakamakon zaben ba, mu jam’iyyarmu masu bin doka da oda ne” in ji shi.
Ya kuma kara da cewa, “Muna amfani da wannan daman na kira ga shugaban hukumar zabe ta kasa INEC, Farfesa Mahmud Yakubu da shugaban hukumar a jihar Kebbi da kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari, musamman ganin bayanan da yake yawan yi na cewa, zai tabbatar da an ba duk wanda ya lashe hakkinsa ba tare da nuna banbancin siyasa ko bangare ba. Muna da tabbacin cewa mun ci zabe saboda haka a zo a sanar mana da nasarar da muka samu, muna da mazabar 8 a wannan yankin an bayar da sakamakon zabe daga mazabu 7 saura gudummar Marafa kadai ta rage kuma mazabar bashi da nisa daga ofishin zabe, bai kai nisan rabin kilomita ba kuma wai an kasa gano jami’in masu tattara sakamakon zaben yankin wai ya bace ba a san inda ya shiga ba, duk da cewa, ita hukumar zabe ta dauke shi aiki, kafin ta dauke shi aiki ya kamata a ce ta sassan cikakken adireshinsa, kuma mutum ne ba aljani ba ne, akan haka muke kira da gaggawa kuma da babbar lafazi a kan cewa a gaggauta fadin sakamakon zaben da aka yi na yankin Kebbi central, kuma du kwai shiri ko kutungwuila, ko wani hauma-hauma da ake shirya muna da labari, duk inda aka kuskura aka kaucewa tsari da aka yi to wallahi za a ga abin da aka biyo baya za a ga abin da zamu yi, inda aka dauki doka a hanun muna zamu dauka, bamu fatan mu yi muna kada ayi mana”.