Iyalan wani jami’in sibil difens mai suna DSP Adama Adekunle Emmanuel, mai shekaru 45, sun ce suna zargin abokin aikinsa ne ya harbe shi har lahira a ranar Lahadi a wani otel da ke Abuja.
Matar marigayin ta ce alamu sun nuna an kashe mijinta ne, saboda an samu raunukan harbin bindiga a kafaɗunsa.
- Gini Ya Rushe A Jigawa, Mutum 1 Ya Rasu, 7 Sun Jikkata
- Kasar Sin Ta Bayar Da Gaggarumar Gudunmuwa Ga Wanzuwar Zaman Lafiya Da Ci Gaba Mai Dorewa A Duniya
Ta kuma bayyana cewa an ba su labarai daban-daban uku kan yadda aka ce mijinta ya mutu, lamarin da ya sa suke zargin ana ƙoƙarin rufe gaskiyar abin da ya faru.
Kakakin rundunar ’yansandan birnin tarayya, Josephine Adeh, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce jami’an tsaro na ci gaba da bincike domin gano gaskiya.