Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Carlo Ancelotti ya kafa tarihi bayan da kungiyar tasa ta je ta doke Espanyol da ci 3-1 a wasan mako na uku a gasar La Liga da suka fafata ranar Lahadin da ta gabata.
Minti 12 da fara wasan dan wasa Binicius Junior ya ci wa Real Madrid kwallonta, sai dai sauran minti biyu su je hutu mai masaukin baki kungiyar Espanyol ta farke kwallon ta ta hannun dan wasa Joselu.
- Ba A Kai Wa Kwankwaso Hari A Kogi Ba – Kungiyar Yakin Zaben KwankwasoÂ
- Za Mu Taimaka PDP Ta Fadi Zaben 2023 -Wike
Har ila yau saura minti biyu a tashi daga wasan Real Madrid ta kara kwallo ta biyu ta hannun kaftin dinta Karim Benzema, sannan ya kara ta uku kuma ta biyu a wasan dab da alkalin wasa zai tashi.
Wasan dai shi ne na 179 da Carlo Ancelotti ya ja ragamar Real Madrid, sannan ya hau kan Jose Mourinho a jerin wadanda suka ja kungiyar wasanni da dama sannan cikin wasannin Ancelotti ya samu nasara a wasanni 132 da canjaras 22 da rashin nasara 25.
Hakan yana nufin shi ne na shida a jerin wadanda suka ja ragamar kungiyar wasanni da yawa, ya haura tsohon kociyan kungiyar Jose Mourinho wanda ya yi wasanni 178 kuma wadanda ke gaban Ancelotti sun hada da Miguel Munoz mai wasa 605 da Zidane da ya ja ragamar karawa 263 da Del Boskue mai 246 da Beenhakker 197 da kuma Molowny da ya ja ragamar wasannin Real Madrid wasanni 183.
Cikin wasanni 179 da Ancelotti ya ja ragama sun hada da 117 a La Liga da 38 a Champions League da 16 a Copa del Rey da hudu a Spanish Super Cup da wasa biyu a Club World Cup da kuma biyu a European Super Cup.
A matakinsa na kociyan Real Madrid ya lashe kofi takwas a kungiyar da suka hada da Champions League biyu da Club World Cup daya da European Super Cups biyu da LaLiga daya da Copa del Rey daya da kuma Spanish Super Cup guda daya.