Ministan kula da sufuri na kasar Angola, Ricardo de Abreu, ya bayyana gamsuwa da aikin kamfanin kasar Sin da aka ba kwangilar gina sabon filin jirgin sama a babban birnin Luanda na kasar, inda ya yaba da ingancin aikin.
Ministan ya bayyana haka ne jiya, lokacin da ya raka shugaban kasar Joao Lourenco rangadi a filin jirgin sama na kasa da kasa na Dr. Antonio Agostinho Neto, wanda kamfanin AVIC-ENG na kasar Sin ke ginawa.
Ministan ya kuma bayyana muhimmancin da sabon filin jirgin saman ke da shi wajen habaka tattalin arzikin kasar a bangarori daban-daban, yana mai jaddada cewa, ababen more rayuwa su ne ginshikin bunkasar bangarorin bude ido da masana’antu da aikin gona da kiwon kifi.
Ya ce filin jirgin saman na iya zama cibiyar jigilar kayayyaki da zai bunkasa ci gaban tattalin arziki a kudu maso yammacin Afrika.
Da yake bayyana yadda kasashen biyu ke da alaka ta kut da kut da hadin gwiwa, ministan ya ce Sin ta bayar da gudunmuwa mai karfi wajen sake fasalin Angola da raya ababen more rayuwa da bunkasa tattalin arzikin kasar. (Fa’iza)