Assalamu alaikum wa rahmtullah. Masu karatu, a makon da ya gabata, muna bayani ne a kan wani malami daga cikin Falasifawa wadanda suka sa kwakwalwa suka yi tunani suka gwada abubuwa suka tankade suka rairaye suka fadi abin da gaskiya ta nuna masu game da Manzon Allah (SAW). Kamar yadda muka fada, su ba ruwansu da wani bangare na addini, bare su ji tsoron fadar duk wata gaskiya, kada a ce sun taba addinin wani, ba ruwansu da bangaren wata jama’a, su hadimar ilimi ne, ilimi suke yi wa hidima. Su idan ilimi ya yadda da wani abu sun gwada sun gani to ko zai zama a bakin ransu za su fada, za su fito da abin da wannan ilimi ya ba su.
Shi wannan ya gwada mazaje ya gwada Annabawa da aka fada, ya gwada duk wasu mazaje da suka yi tashe duk ga baki daya har ya zo ya gwada Annabi (SAW), ya dora shi kan sikeli irin nashi, ta ko wanne bangare, sai ya cimma matsayar cewa ba shugaba mai girman Annabi Muhammadu (SAW), mu kuma mu ce Annabi (SAW), shi ne mai girman duk wani mai girma da Allah ya taba yi. Duk wani babba tun da aka fara tarihi har ya zuwa zamanin Manzon Allah (SAW) har ya zuwa zamanin shi masanin, wajen 1930 (wanda ya yi wannan littafin) ya ce Manzon Allah (SAW) shi ne mai girma, mai daraja mai daukaka, madaukakin duk wani mai daukaka da aka taba yi.
- Masu Kallon Fina-Finai Na Sin Sun Gamsu Da Fina-Finan Da Aka Gabatar A Lokacin Hutun Bikin Murnar Ranar Kafuwar Sabuwar Kasar Sin Ta 2025
- Sin Na Ci Gaba Da Goyon Bayan Kawo Karshen Rikicin Gaza
Manzon Allah (S.A.W) shi ne Annabin annabawa, malamin malamai. Wannan Bafalassafe da ya auna Annabi (S.A.W.) ya auna komai nasa, ilimi da babu ruwansa da addini bare ya ji tsoron fadar wata magana ko yana tsoron wuta, ba wuta ba aljanna shi a gabansa kawai gaskiya a fade ta yake cewa Manzon Allah (S.A.W.) shi ne mai girma, shi ne mai darajar duk wani dan adam da Allah ya yi masa rai, to ka ga shugabannin ’yan adam din ma kamar yadda muka fada wadanda su ne Annabawa (A.S.W.), ba dan Manzon Allah ba da ba a nada su ba inji {ur’ani kamar yadda ayar cikin Suratu Ali Imrana ta nuna cewa, Allah ne ya riki alkawarin Annabawa, Allah ne ya rattaba hannu ga Annabawa.
Ga alkawarin, komai da Allah Ya yi wa wani, Allah Ya fada. Allah bai boye komai ba, sai abin da ya yi ga Annabi Muhammadu (S.A.W.), nan ko ba a fada ba, amma kowane annabi komai matsayinsa in ka duba sai ka ji sirrin da aka yi da shi. Yanzu game da wannan ma’aiki da annabawan da duk Allah ya tara su, ga abin da Allah Ya ce (ya ku) Annabawa, idan na ba ku littafanku da kyawawan dabi’u da hikima da ma’arifanku (ai, misali, an ba ka wukar yanka da takobin yanka da tagwayen masu ke nan). Sannan wani ma’aiki ya zo maku (Manzon Allah ake nufi) za ku bar wannan sakon da wannan nadin da na yi maku ku yi imani da shi kamar mutan Makka muhajirun, za ku taimake shi kamar mutanen Madina, ku tabbatar kun yi furuci a kan wannan. Annabawa suka ce mun tabbatar ya Ubangiji, Allah Ya ce to na ji, a shaida, yanzu kowa ya sa hannu ni ma kuma zan sa hannu.
Wani malami yake cewa in dai lamarin Manzon Allah (S.A.W.) ne wani baki ma bai iya fada, kamar za ka iya cewa komai Allah kan dauke shi yadda ya dauke shi, amma idan abin Manzon Allah ne Allah bai daukar shi da wasa.
Ayar ta yi gargadi a kan kar wani (a cikin Annabawa) ya juya baya ga wannan alkawarin da Manzon Allah ya zo da shi, ya ki tashi daga annabtarsa, ya ki bin Manzon Allah. To ka ga ashe Manzon Allah (S.A.W.) shi ne Annabin Annabawa, shi ne ma’aikin ma’aika, manzon Allah shi ne mafi girman duk wani mai girma na halittar Allah.
Manzon Allah (S.A.W.) shi ne mafi girman wani mutum da tarihi ya sani, shi wannan masanin falsafa da ya fadi wannan kusan ya karanta tarihin duniya tun daga farko har karshe, yana da tarihin duniya domin malami ne masanin falfasafa da ya yi bincike kwarai kuma ba shi da wani addini da zai hana shi karanta wannan. Ya nuna idan muna son mu karanta wani abu watakila muna tsoro saboda addini, shi ko ba shi da wannan (addini) ma, yake cewa “Manzon Allah (S.A.W.) shi ne mafi girman wani dan Adam da tarihi ya sani, shi ne wanda ya juya halitta ya kawo wa halitta canji, ya kawo mata canji cikin addini da yadda duk ake addini, a zo da addini ta kowane fanni sai Manzon Allah (S.A.W.).
Masanin falsafan ya ce Manzon Allah ya kawo canji a cikin addini, ya kawo canji cikin siyasa, da tsarin rayuwa, da tsarin kasa, da tsarin jama’a. Manzon Allah (S.A.W.) Annabi ne, ma’aiki ne daga Allah, Annabi ne, ma’ana malami ne wanda ya yi karatu a Hadarar Allah, ma’aiki ne, ma’ana ma’aiki ne ba kamar yadda muke dauka kamar wani dan sako ba, saboda galibi wasunmu abin da muka sani da an batun manzo sai a dauka dan aike ne kawai mai isar da sako ko ya karanta, amma ma’iki abu ne mai girma na daga annabawa, mutum ne da ya yi fikiri, ya yi tunani har ya samu saduwa a cikin hadarar Allah, har ya zama ma’aiki a hadarar Allah.
Yanzu duk abin da zai fada Hadarar Allah ce ta sa shi, siyasa ce da Hadarar Allah yake fada, Hadara ce ta sa shi ya fada, su sauran annabawa dukkansu Allah ya bar masu ladabin su isar da sakon wanda da ma su ma’aikan Allah ne, Annabi Isa ne ya dauke masa wannan ya ba shi izini, shi Annabi Isa ne zai fadi abin kai-tsaye daga Hadarar Allah, cewa Allah ne Ya ce ba wani ma’aiki ko wani abu ba, Annabi Isa ne kadai ke da wannan, amma sauran Annabawa dukanninsu za su ce ma’aikin Allah ne, kar ka za ci wani abu ne na wulakanci, a’a abu ne da ke da girma, saboda Manzon Allah ya yi fikiri, ya yi tunani ya yi halwar da duk wani mai takamar halwa zai yi, ya shiga inda duk wani dan tunani ke takamar ya shiga.
Annabi (SAW) ya shiga kogon hira ya yi adadin kwanaki, ya yi adadin watanni, duk malamai sun tafi ba sallah ya je ba, tahamusi ya rika yi, kamar yanzu mutum ya shiga kogo na dutse ka kulle kanka na tsawon kwanaki arba’in (40) ai ka cika namiji bare ka tafi daji-dajin ma ka hau dutse, dutsen ma ka shiga cikin kogo, Allah ya san me ye a cikin kogon nan. A zamani irin na wannan lokaci, har Allah ya ba Manzon Allah (SAW) abin da ya ba shi, dan haka mun gode wa Allah.
Duk annabawa fa ba wasa ba ne, kowane a cikinsu sai ya yi tunanin nan. Annabi Ibrahim ya yi tunanin nan, Allah Ya yaye masa malakutus samawati Wal’ ard. Annabi Musa (AS) wannan ciwon da ya yi shekaru arba’in (40) a cikin yawon neman Allah ya yi, amma duk da haka sai ka ga ya iya abin da Allah ya ba shi ga shi da wani a cikin jama’arsa ko zamaninsa zai yi wani tunani babba har ya iya gano wani abin da al’imma za ta ki yarda da wannan abu in ya yi wasa ma ta kashe shi. Amma Manzon Allah da tafakkurinsa zikirinsa da shiga cikin kogo da shafewarsa da haduwarsa da mudalakin hakika da Manzon Allah (S.A.W.) babu wani dan halitta da ya isa ya ce zai yi irin wannan har ya zo da abin da annabi ya zo da shi (S.A.W.), babu shi.
Shehi babbanmu, Ibn Arabi Hatimi duk abin da zai rubuta a cikin Futuhatil Makiyya da Khususil Hikam zai ce “ni fa magaji ne na manzon Allah, ban yi kusa ma da Manzon Allah (S.A.W.) ba, gado ne”, kuma da gaske yake yi. Shehu Ibrahim Inyass (R.A.) ya ce duk abin da ya fada, ya fada ne saboda shi Hadimin Manzon Allah ne, ya ce Manzon Allah ne ya ba ni, ya yi mani wata kyauta ta daban, bayan baiwar can, ya kuma ba ni abin da ma bai ba halitta ba, amma komai girman abin na Shehu Ibrahim ya ce Manzon Allah ne ya ba shi.
Duk irin wannan ilimi na Sayyidina Ali wanda ya bugi kirji ya ce ni ne digon nan na karkashi ba’un, amma duk wanna sunansa kofar ilimin Manzon Allah, amma gidan ilimi shi ne Manzon Allah (S.A.W.), saboda haka mu daina tsoro, malamai na musulunci su daina tsoro, ba wani wanda zai zo da wani karatu, ba wani wanda zai fito da wani abu wanda ya fi karfin na Annabi din nan (S.A.W.), a’a duk abin da zai zo da shi a cikin na Manzon Allah (S.A.W.) ne.