Kadan daga cikin matsalolin dake addabar mata musamman yara, matasa, ita ce tura su aikatau wassu garuruwa ba tare da la’akarin wadanne irin matsaloli za su fuskanta a can ba.
Iyaye kan tura yara mata wasu garuruwa da sunan neman kudi ko samo abin duniya, wanda kafin a samu yaro namiji daya da aka tura aikatau sai an samu yara mata sama da goma da aka tura, me ya sa?
Yana da kyau iyaye mata su fahimci cewar ‘ya mace abar tattali ce da kulawa, tana bukatar tallafi fiye da namiji ta kowacce fuska amma iyaye ba sa duba haka.
Wasu iyaye dai bukatarsu a sama musu kudi ta kowacce hanya.
Me ya sa iyaye ke tauye rayuwar ‘ya mace? Me ya sa ba za a ba ta dama ba ta yadda za ta kula da rayuwarta da na yaran da za ta haifa a gaba ba? Inda a ce za a ba wa yara dama a ji ta ra’ayinsu fiye da rabinsu ba wai suna so ba ne ake tura su wannan aikatau din.
Matsalolin Da Tura Yara Mata Aikatau Ke Haifarwa Akwai matsaloli da tura yara mata aikatau ke haifarwa masu tarin yawa amma ga kadan daga cikin su:
1: Yana hana ta neman ilmi.
2: Yana dakushe mata mafarkinta ya hana mata cikar burinta.
3: Yana bata tarbiyya.
4: Yana mayar da ita marar ‘yanci.
5: Yana mayar da ita tamkar baiwa
6: Yana haifar da rashin tausayi a zuciyarta. Ta yadda za ta sa a ranta cewar ba a sonta ya sa aka kai ta wani wuri da sunan aiki wannan dalili sai ya kangarar mata da zuciya.
7: Yana jefa yara harkar sace -sace.
8: Wasu na fadawa harkar zinace-zinace.
9: Karshe wasu su dawo gida da ciki hade da ciwon zamani.
Ina Mafita?
Mafita a nan ita ce:
1: Iyaye mu sani cewar duk kudin da za a yi nema ta wani gari to ana iya samunsa a gida.
2: Mu tabbata in zamu tura yara aikatau a yi yarjejeniyar ba su damar neman ilmi.
3: A rinka bibiyar halin da suke ciki a kodayaushe.
4: Mu saurare su a lokacin da muka kai musu ziyara ta nan za mu fahimci matsalarsu.
5: Mu rinka tuntubar su ta wayar hannu mu ji labarinsu.
6: Idan sun zo ganin gida mu tabbatar da mun bincike su.
7: Mu sa ido sosai don ganin halayyarsu ba ta canja ba.
8: Idan da hali mu kyale su su yi aikin kusa da mu muna ganin shiga da fitar su.
Shawara
A shawarce yana da kyau iyaye mu sa ni cewar babu alheri wurin tura yara aikatau wasu garuruwa, yara mata da yawa kan fada garari da kuncin rayuwa a lokacin da suka bar gaban iyayensu da sunan neman kudi a wurare dabandabam. Mu sani daraja da mutunci hade da rayuwar yaranmu sun fi mana komai a rayuwa. Iyaye mata a kula da wannan.