Kungiyar Jam’iyyatu Ansariddeen Attijjaniyya ta raba wa mutanen da harin bam ya jikkata a Garin Tudun Biri kayayyaki da kudade da asibitocin da aka kwantar da su a Jihar Kaduna.
Kungiyar ta kai wannan ziyara ce karkashin jagorancin Sheikh Muhammad Abdul’ahad Ibrahim Niass tare da sauran shugabannin kungiyar, kamar babban sakatare, Muhammad Al-Kasim Yahaya da daraktan ayyuka, Muhammad Muhammad Nasiru Hamisu da sauran mambobi da dama.
- Tinubu Ya Sake Mika Ta’aziyyarsa Ga Iyalan Da Harin Bam Ya Rutsa A Tudun Biri, Kaduna
- Jama’ar Tudun Wada Na Zanga-Zanga Kan A Yi Adalci A Zargin Kisa Da Ake Wa Doguwa
Sun dai halarci asibitocin 44 da na Barau Dikko da ke Kaduna domin ganin halin da majinyatan suke ciki da kuma raba musu wadannan kayayaki. wanda ya Faru a Garin Tudun Biri Jihar Kaduna.
kungiyar dai ta raba atamfa 150, jallabi na maza 100, dinkakkan kayan mata 50, dinkakkan kayan maza 70, takalma silifas 100, sabulun wanka da dama 7, da kuma tsabar kudi na naira 10,000 ga mutun dari da ashirin.