Wasu ‘yan bindiga sun sake yin garkuwa da hakimin Garu Kurama da ke ƙaramar hukumar Lere a jihar Kaduna, Yakubu Jadi, da ɗiyarsa Malamar Cocin Katolika da wasu mutane huɗu a ƙauyen Gurzan Kurama.
Duk da cewa rundunar ‘yansandan Kaduna ba ta tabbatar da faruwar lamarin ba, har ya zuwa lokacin tattara wannan rahoto, ƙungiyar jama’ar Kudancin Kaduna (SOKAPU), ta hannun jami’inta na hulda da jama’a Josiah Abraks, ta bayyana cewa an yi garkuwa da mutanen ne a daren Juma’a, 23 ga Agusta, 2024, amma har yanzu ‘yan bindigar ba su nemi dangin waɗanda sukai garkuwa da su ɗin ba.
- ‘Yansanda Sun Cafke ‘Yan Uwan Da Suka Birne Matashi Da Ransa A Kaduna
- Wace Wainar Ake Toyawa A Jihar Kaduna?
SOKAPU, ta bayyana lamarin a matsayin abin takaici da ban tsoro tare da kira ga hukumomin tsaro da sauran wanda abin ya shafa da su yi iyakacin ƙoƙarinsu wajen ganin an sako waɗanda aka yi garkuwa da su ɗin cikin gaggawa.
Kazalika ta buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta ƙara ƙaimi wajen kare rayuka da dukiyar al’umma inda ta buƙaci jama’a da su kasance masu taka-tsan-tsan tare da sanar da hukumomin tsaro duk wani motsi ko yunƙuri da ba su a saba gani ba.