Jam’iyyar APC ta zargi jam’iyyar PDP mai mulki a Jihar Filato kan shirin yin amfani da addini don samun nasarar siyasa a zaɓen gwamna na 2027.
Zargin ya fito ne a daidai lokacin da jam’iyyar APC keke ƙoƙarin ƙwace iko a jihar a 2027. Idan za a iya tuna dai a halin hanzu, shugaban jam’iyyar APC, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya fito ne daga Jihar Filato, wanda hakan ta ƙara zazzafar siyasar jihar, inda APC ke ƙoƙarin lallai sai ta amshi mulkin jihar a 2027.
APC ta zargi PDP da cewa tana ƙoƙarin raba kan Musulmai a jihar tare da ƴ an asalin da wadɗanda ba ƴ an asalin jihar ba domin ta ci gaba da mulkin jihar ta kowane hali.
- 2027: Su Wane Ne Ke Tsoron Guguwar Makinde A Jam’iyyar PDP
- Tsohon Mataimakin Gwamnan Gombe Da Wasu jigogin PDP Sun Koma APC
Muƙaddashin mai magana da yawun APC a jiha, Shittu Bamaiyi, wanda ya yi iƙirarin a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya kuma ce PDP tana ƙoƙaƙin yin amfani da wannan dabarar ce saboda ta kusa rasa iko a fagen siyasar jihar.
“Akwai tsananin damuwa da fargabar a cikin harkokin siyasar Jihar Filato, domin kuwa PDP ta zaɓi wasu sabbin dubaru da za su ba ta damar ci gaba da mulki ko da kuwa sun saɓ awa doka.
“A wani ɓangare na wannan dubarar, jam’iyyar a ƙarƙashin kulawar ɗaya daga cikin manyan ma’aikatan gwamnati, ta yi ƙoƙarin shirya zaɓen jagoranci ƙungiyar Musulmai ƴ an asalin Jihar Filato a cibiyar Azi Nyako da ke Dadin-Kowa a garin Jos, wanda daga bayanan da aka samu lamarin ya kasa samun nasara.
“PDP na ganin cewa da wannan dubarar na raba kan Musulmin Jihar Filato za ta iya samun nasara a zaɓen 2027, wanda wannan ka iya kawo rashin jituwa da haɗin kan al’umma, musamman a irin wannan lokaci da ake fama da rikice-rikice addini da ƙabilanci da kuma ayyukan ƴ an ta’adda, wanda hakan bai kamata a siyasantar da addini ba.
“Yadda PDP ke amfani da addini a matsayin hanyar lashe zaɓe, tana sake dawo da amfani da siyasa mara tsafta wajen lashe zaɓen 2027 da kowacce hanya,” in ji mai magana da yawun APC.
Amma shugaban PDP na yankin tsakiyar Nijeriya, Monday Daspan, ya musanta wannan zargin a matsayin wanda ba shi da tushe ballantana makama.
“Bamaiyi ya shigo harkar siyasa ta bayan fage ba hanyar da ya kamata ba. Wannan shi ne dalilin da ya sa hakan ya yi masa sauƙi wajen gwama addini da harkokin siyasa. Mafi yawan waɗanda suka shigo harkar siyasa ta bayan fage ba su da cikakken ƙwarewa wajen yin magana a cikin harkokin siyasar ƙasar nan.
“Mu a matsayinmu, APC ba za su iya daidaita tsakanin mulki da ci gaba ba. Sun yi rashin nasara kan zaɓe kuma suna son danganta shi da wani abu. Matsalar a nan dai ita ce, Gwamna Celeb Mutfwang yana aiki ko kuma ba ya yi? Eh. Shin Lalong ya yi aiki da ya yi? A’a,” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp