Jam’iyyar haɗaka ta ADC ta bayyana cewa APC na ƙoƙarin tarwatsa ta ne saboda kar ta ƙwace mulki a 2027, wanda ya sa take janyo rikici da tsorata ‘ya’yan jam’iyyar da take ganin shi ne mafita a gareta.
Idan za a iya tunawa dai ƴan daba sun tarwatsa taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar ADC a Jihar Kaduna a makon da ya gabata.
- DAPPMAN Ta Soki Matatar Dangote Kan Rage Farashin Man Fetur
- ADC Ta Bukaci Tinubu Ya Kafa Dokar Ta Baci A Katsina Da Zamfara Kan Rashin Tsaro
Haka nan, taron shugabannin ADC a Jihar Legas a ƙarshen mako ya zama tashin hankali bayan an kai hari ga mahalarta taron da ake zargin ‘yan daba ne suka kai hare-hare da nufin tarwatsa taron. Wannan lamari mai tashin hankali ya faru a lokacin da Gbadebo Rhodes-Viɓour, wanda shi ne ɗan takarar gwamna na jam’iyyar LP a Legas a shekarar 2023, ya canza sheka zuwa ADC.
An bayar da rahoton cewa yawancin ‘yan daban siyasa sun mamaye wurin taron a Alimosho, inda za a fara bayyana Rhodes-Viɓour a matsayin sabon mamba na ADC, bayan rufe wuri na asali da aka shirya taron a Lion Field, da jami’an tsaro suka yi.
Mai magana da yawun jam’iyyar ADC, Malam Bolaji Abdullahi, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce harin da aka kai a Legas ya nuna irin mulkin zalunci na jam’iyyar da ke mulki wadda ta nuna wa ƴan adawa a cikin makon da ya gabata.
ADC ta ce, “APC tana tsoron ƙaruwar shaharar ADC a faɗin ƙasar nan ne, kuma yana bayyana cewa shi ne kawai hanyar da za su iya bi wajen tarwatsa ƴan adawa a ƙasar nan.
“An fara ne a Jihar Edo da gargaɗin shugabannin ADC kan ka da su ziyarci jihar, sannan Kogi ta biyo baya, tare da rufe tashar rediyo ta kashin kai a Jihar Neja, kafin ya ƙaru zuwa ga kai hare-haren da aka ɗauki nauyi kan taronmu na Kaduna, sannan kuma da hare-hare a kan ayarin motocin shugabannin ADC a Kebbi.
“Haka kuma an kai hari a wurin taron ADC a Alimosho a Jihar Lagos, wannan yana nuna cewa APC ta ji kunya kuma ba ta girma ko kaɗan. A ƙarƙashin gwamnatin APC, rundunar ‘yansandan Nijeriya ta zama wani sashi nak are jam’iyyar mulki.
“Bisa ga waɗannan hare-haren da ake kai mana, babu wanda zai iya hasashen cewa wannan gwamnati na APC da ke ƙarƙashin shugaban ƙasa Tinubu za ci gaba da zama a kan mulki har na tsawon shekaru 8.
“Yanzu, ƴan daban da APC ta ɗauki nauyinsu sun kai hari a coci. Idan cocin da sauran wuraren ibada ba a ɗauke su a matsayin wuraren da ba za a taɓa iya kai hari ga APC ba, ta yaya jam’iyyar za ta iya tabbatar wa duniya cewa ba gaskiya ba ne ba ta cikin ƙungiyoyin ƴan ta’adda. Bayan haka, harin wuraren ibada shi ne abin da ƴan ta’adda ke yi.”
Duk da haka, ADC ta yi barazanar cewa, “Ba za mu zauna muna kallon ana kai wa shugabanninmu da wuraren taronmu hare-hare ba ƙaƙƙautawa ba. Dole ne mu ɗauki matakin dakatar da lamarin. Cikin gaggawa ba tare da ɓata lokaci ba.”
Amma yake mayar da martani, daraktan yaɗa labarai na APC na ƙasa, Bala Ibrahim, ya karyata wannan zargin, yana cewa jam’iyyar da ke mulki ba ta da hannu wajen kawo rikici a jam’iyyun adawa. Har ila yau, ya ce ADC ba barazana ce ga APC ba, yana mai jaddada cewa jam’iyyar da ke mulki ba ta yarda da duk wani tashin hankali ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp