Jam’iyyar APC reshen jihar Kebbi ta bukaci hukumar zabe mai zaman kanta da ta fitar da sakamakon zaben mazabar majalisar dattawan Kebbi ta Arewa da na majalisar wakilai na mazabar tarayya ta Areaw- Dandi.
Jami’in hulda da jama’a na jam’iyyar (PRO) Alhaji Isah Asalafi ne ya yi wannan roko yayin ganawa da manema labarai a Birnin Kebbi. Ya ce “APC na sa ido ga INEC da ma daukacin al’ummar jihar da kuma m barin su cikin duhu don sanin abin da ke faruwa game da sakamakon zaben. Don haka tare da mutunta ga hukumar zabe don tabbatar da cewa ba a sauya sakamakon zaben ba.
Ya kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC da magoya bayansu da masu hannu da shuni da kada su dauki doka a hannu su da su baiwa hukumar zabe damar yin abin da doka ta shata. Muna matukar godiya ga daukacin masu zabe a jihar Kebbi da ma kasa baki daya da suka fito gangamin zaben Asiwaju Bola Ahmed Tinubu wanda ya bashi nasara a matsayin zababben shugaban kasa.
A cewarsa, har yanzu ba a kammala zaben ba, domin zaben gwamna da ke tafe nan da makonni biyu masu zuwa, ya kamata masu zabe su dukufa wajen zuwa ranar tare da kada kuri’unsu ga daukacin ‘yan takarar gwamna na jam’iyyar APC a dukkan jihohin kasar nan.
Ya kuma yi nuni da cewa, wasu sakamakon zaben da hukumar zabe mai zaman kanta ta bayyana a jihar, jam’iyyar da kuma kungiyar lauyoyin ta na nazarin yadda zaben ya kasance.
Haka kuma, bayan nazari idan har ya sa jam’iyya ta yi ikrari ko tambayar sakamakon zaben, za mu yi hakan ne a kotun sauraron kararrakin zabe, don haka muna kira ga al’umma su kantar da hankalinsu jam’iyyar na iyakacin kokarin ganin an yi adalci.
Ya kara da cewa, jam’iyyar za ta shirya wani gangami a jihar domin nuna wa al’amuransu na nasarar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da kuma nuna wa jam’iyyar adawa, APC ce mai mulki a jihar da kuma kasa baki daya,inji Alhaji Isah Asalafi.