Jam’iyyar APC ta kasa ta dauko manyan lauyoyi (SAN) da za su kare nasarar da zababben shugaban kasa mai jiran gado sanata Bola Ahmed Tinubu ya samu a zaben ranar 25 ga watan Fabrairun, 2023.Â
Lauyoyin za su kare nasarar da Tinubu ya samu a lokacin zaben a gaban kotun da za ta saurari korafe-korafen sauran ‘yan takarar da basu samu nasara a zaben ba.
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP Atiku Abubakar da takwaransa na jam’iyyar LP Peter Obi, sun ki amincewa da sakamakon zaben inda suka kalubalanci sakamakon zaben a gaban kotun daukaka kara.
A zaman da kotun ta yi a makon da ya gabata, ta ba masu shigar da karar damar duba kayan da INEC ta yi amfani da su wajen gudanar da zaben.
Acikin wata sanarwa da mai ba Jam’iyyar APC shawara kan harkokin shari’a, Ahmad Usman Almarzuq ya fitar a ranar Talata, ta bayyana yadda jam’iyyar ta kaddamar da kwamiti mai Mutum 13 ciki har da manyan Lauyoyi 12 da zasu kare nasarar da Tinubu ya samu.
Sanarwar ta ce, SAN Prince Lateef Fagbemi ne zai jagoranci kwamitin musamman ganin cewa, ya yi fice wajen jan ragamar kararrakin zabe.
Sauran mambobin kwamitin sun hada da Ahmad Usman El-Marzuq, Sam Ologunorisa, Rotimi Oguneso, Olabisi Soyebo, Gboyega Oyewole, Muritala Abdulrasheed, Aliyu Omezia Saiki, Tajudeen Oladoja, Pius Akubo, Oluseye Opasanya, Suraju Saida da kuma Kazeem Adeniyi.
Sanarwar ta ce, APC na da kwarin guiwa akan kwamitin musamman ganin cewa suna da kwarewa wajen jagorarantar kararrakin zabukan shugaban kasa.