Kasa da awa 48 kafin gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da za a yi a ranar Asabar, jam’iyyar APC a Jihar Ribas, ta soki mataimakin Sufeton ‘yansanda, AIG Abutu Yaro da Kwamishinonin ‘yansanda hudu da aka turo zuwa jihar domin sa ido kan zabe saboda ziyarar da suka kai wa gwamnan jihar, Nyesom Ezenwo Wike.
Kwamishinonin da suka hada da Yomi Olanrewaju, Samuel Musa, Lanre B. Sikiru da kuma Aderemi Adeoye.
- Kungiyoyi Magoya Bayan Buhari-Osinbajo Sun Bukaci ‘Yan Nijeriya Su Zabi Atiku Na Jam’iyyar PDP
- An Daure Dan Kamasho Wata 6 Kan Satar Batirin Mota A Abuja
Kakakin kwamitin yakin neman zaben APC a jihar Sogbeye Eli, a hirarsa da manema a yau Alhamis, ya ce, a bisa wannan ziyarar da suka kai wa Wike sun kasance ba su da wani kwarin guiwa a kan ‘yansanda.
Sogbeye ya ci gaba da cewa, Wike da ‘yan barandarsa sun kitsa yadda za su yi magudin zabe, inda ya ce, Wike ya fitar da miliyoyin Naira har da kudaden kasar waje ya raba wa jami’an.
A cewarsa, jami’an sun kuma kasance suna yin sintirin gidan Wike da dare da ke a yankin Rumuepirikom tun a ranar 22 ga watan Fabirairu 2023.
Kakakin ya kuma yi zargin cewa, Wike ya kitsa wani shiri da jami’in tsaro a jihar domin a yi wa shugabanin APC dauki dai-dai a jihar, har da na kananan hukomomi.
Ya sanar da cewa, “Mun samu bayanan sirri daga kananan hukomomin jihar cewa, ana son a dauke shugabanin APC da dama, don a tauye masu ‘yancinsu a lokacin gudanar da zabe.”
Ya buga misali da dauke Victory Agbara a karamar hukumar Tai a ranar 21 ga watan Fabirairu 2023, bayan ya fice daga PDP ya komawa jam’iyyar APC, inda kuma bayan kwana biyu, aka shigar da karar Ogbonna Nwuke a gaban kotu.