Jam’iyyar Action People’s Party (APP) ta lashe kujeru 22 daga cikin kujeru 23 na shugabancin kananan hukumomi a zaben da aka yi ranar Asabar a Jihar Ribas.
Babban jami’in zaben Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Ribas (RSIEC), Mai Shari’a Adolphus Enebeli ne, ya sanar da sakamakon a yammacin Asabar a garin Fatakwal.
- Sin Ta Yi Kira Ga Kwamitin Tsaron MDD Da Kada Ya Yi Watsi Da Bincike Game Da Fashewar Bututun Gas Na Nord Stream
- Rashin Kayan Aiki Kan Sa Muna Kallon Majinyaci Zai Mutu Mu Kasa Taimakon Sa – Dakta Musubahu
Sai dai ba a sanar da sakamakon karamar hukumar Etche ba saboda har yanzu ana tattara sakamakon zaben.
Za a sanar da sakamakon karamar hukumar ta Etche tare da na kujeru 319 na kansiloli nan gaba kadan.
Rahotanni sun nuna cewa gwamnan jihar, Siminalayi Fubara, ya goyi bayan jam’iyyar APP a wannan zabe saboda rikicin da ya barke a jam’iyyar PDP mai mulki a jihar.
Rikicin ya samo asali ne daga rikicin da ke tsakanin Gwamna Fubara da tsohon gwamnan jihar, Nyesom Wike.